Rikici ya dawo ɗanye, ɗan majalisa ya buƙaci Kotu ta soke ɗan takarar gwamnan Kano na APC

Rikici ya dawo ɗanye, ɗan majalisa ya buƙaci Kotu ta soke ɗan takarar gwamnan Kano na APC

  • Mamba a majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar birnin Kano, Sha'aban Sharaɗa, ya nemi Kotu ta soke takarar Gawuna na APC
  • Ɗan majalisar ya ce Ɗan takarar da jam'iyyar APC sun saba wa sabon kundin dokokin zaɓe 2022 a wurin zaɓen fidda gwani
  • A cewarsa wasu masu rike da kujerun siyasa a gwamnatin Kano sun kaɗa kuri'a a wurin zaɓe wanda ya saba wa sashi na 84(13)

Kano - Ɗan majalisa mai wakiltar birnin Kano a majalisar dokokin tarayya, Sha'aban Sharaɗa, a ranar Alhamis, ya buƙaci babbar Kotun jiha ta soke tikitin ɗan takarar gwamna na APC, Nasiru Gawuna.

Premium Times ta rahoto cewa Sharaɗa ya nemi Kotu ta soke takarar Gawuna ne bisa zargin ya saɓa wa sabon kundin dokokin zaɓe 2022.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a mazaɓar Ahmad Lawan ya bude sabon shafi, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Ɗan majalisar, wanda shi ne shugabam kwamitin tsaron ƙasa da fasaha na majalisar wakilai, ya kasance ɗan takara ɗaya tilo da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwanin APC.

Gawuna da Sha'aban Sharaɗa.
Rikici ya dawo ɗanye, ɗan majalisa ya buƙaci Kotu ta soke ɗan takarar gwamnan Kano na APC Hoto: HE Dr. Nasir Umar Gawuna/facebook
Asali: Facebook

Sakamakon zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan Kano karkashin APC ya nuna cewa Sharaɗa ya samu kuri'u 30 yayin da Gawuna ya samu kuri'u 2,289.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana jam'iyyar APC reshen jihar Kano da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a matsayin waɗan da yake ƙara, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai shigar da ƙaran ya nuna damuwa kan yadda aka bar masu rike da muƙaman siyasa a gwamnatin jihar Kano suka kaɗa kuri'a a wurin zaɓen fidda gwanin.

A cewarsa, hakan ya saɓa wa sashi na 84(13) na kundin dokokin zaɓe wanda ya haramtawa duk me rike da kujerar siyasa yin zaɓe.

Kara karanta wannan

Duk da Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwani, Shugaba Buhari ya faɗi ɗan takarar yake so ya gaje shi a APC

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Alƙalin Kotun mai shari' Liman M. ya karɓi korafe-korafe biyu da mai gabatar da ƙara ya shigar, ɗaya daga ciki shi ne izinin sanar da Gawuna batun ƙarar ta hanyar da ta dace.

Lauyan Sharaɗa ya yi zargin cewa Gawuna ya samu sakon ƙarar amma ya yi kunnen uwar shegu da ita, ya ƙi amsar sanarwar da aka tura masa.

Haka nan kuma Kotun ta ƙarbi bukatar mai ƙara ta biyu na rage zaman Shari'ar daga kwana 30 zuwa kwanaki 15 domin Kotun ta samu damar hanzari kan matakan.

Bayan haka, Kotun ta umarci waɗan da ake ƙara su hallara a gabanta nan da kwanaki 15 domin kare kan su daga tuhumar da ake musu.

A wani labarin na daban kuma Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu kuɗaɗe

Yayin da yajin aikin ASUU ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, wani ɗan majalisa a jihar Kuros Riba ta tausaya wa halin da Lakcarori ke ciki.

Kara karanta wannan

Ekiti: Na yi farin ciki abubuwa sun fara gyaruwa a APC, Shugaba Buhari ya magantu

Mamba a majalisar dokokin jihar, Mista Hilary Bisong, ya tallafawa Lakcarori yan asalin mazaɓarsa da kudi N900,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262