2023: Mambobin jam'iyyar PDP sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Ogun

2023: Mambobin jam'iyyar PDP sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Ogun

  • Mamabobin jam'iyyar hamayya PDP sama da 5000 sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a jihar Ogun
  • Gwamna Dapo Abiodun, wanda ya tarbi masu sauya sheka, ya ce sabbin tsarukan da gwamnatinsa ta zo da shi suna jan hankalin mutane zuwa APC
  • Ya bukaci tsofaffin ƴaƴan PDP su tabbata kowanen su ya mallaki Katin Zabe don ya samu damar sauke nauyin da ke kansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Yayin da ake tunkarar babban zaben 2023, aƙalla mambobin jam'iyyar PDP 5,000 ke suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ogun.

Masu suaya shekan waɗan da mambobin wani tsagin PDP ne a Iperu, ƙamar hukumar Ikenne, sun samu kyakkyawar tarba daga gwamna Dapo Abiodun, ranar Laraba.

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.
2023: Mambobin jam'iyyar PDP sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Ogun Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa a wani taron siyasa da suka gudanar a Oja-Ale, Iperu-Remo, masu sauya sheƙan sun bayyana cewa ayyukan gwamna Nagari ne suka jawo hankalin su suka ɗauki matakin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa a babban ɗan sanda a Nasarawa, sun bukaci Miliyoyi

Mun zama ɗaya da ku - Gwamna Abiodun

Da yake tarban tsofaffin mambobin PDP, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya gode wa yan siyasan bisa ɗaukar matakin shigowa jam'iyya mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce tafiyar da mulku ba nuna banbanci da tsarin buɗe kofa ga kowa da gwamnatinsa ta zo da shi ya jawo mambobin jam'iyyun siyasa da dama sun shiga APC.

Gwamnan ya ce:

"Ina son tabbatar muku da cewa kun zama ɗaya da kowane mamba a jam'iyya. Wannan gwamnatin ku ce kuma a shirye muke mu ba kowa gurin zama don haɗa hannu wajen kawo cigaba ga jihar mu."
"Jam'iyyar mu ta maida hankali wajen gyara jihar Ogun, tun farkon zuwan gwamnati mai ci ta aiwatar da ayyuka a ɓangarori da dama na cigaba da suka haɗa da gina hanyoyi, gyara asibitoci, tallafawa matasa da sauran su."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Akwai matsala' Shugaban APC na ƙasa ya magantu kan ficewar Sanatoci daga jam'iyyar

"Zaɓe na zuwa shekara mai zuwa, ina son kuje ku mallaki katin zaɓe domin da wannan katin ne zaku sauke nauyin dake kan ku na zaɓen waɗan da kuke so su shugabance ku."

A wani labarin kuma Kwanaki kalilan bayan ficewa daga PDP, Tsohon Minista ya sa labule da gwamna Wike

Kwanaki kaɗan bayan ya yi murabus daga PDP, Tsohon ministan Neja Delta, Chief Orubebe, ya gana da gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Taron mutanen biyu ya gudana ne a gidan Wike dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas kuma a sirrance, ba su ce komai ba bayan fitowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262