Ina da tabbacin zan lallasa Atiku, Tinubu da Kwankwaso na ɗare mulki a 2023, Ɗan takara
- Ɗan takarar jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya ce yana da tabbacin shi ne kan gaba da zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023
- Ya ce ba ya tsoron kowane ɗan takara da ake ganin zai iya ba shi matsala, a cewarsa yan Najeriya sun san abinda suke yanzu
- Ya kuma musanta rahoton da ake yaɗa wa cewa ba ya biyan haraji da kuma zargin yana da tabon cin hanci da rashawa
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya ce yana da tabbacin ba tantama zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Laraba, Kachikwu, ya ce ba ya tsoron manyan yan takarar da ke gabansa, waɗan da a cewarsa suke sakin baki ba tare da cika wa ba.
A kalamansa ya ce:
"Wannan dogon tsere ne, wanda ake yaɗawa a labarai ba shi ne zai yi nasara ba a yanzu domin nan da watanni Takwas mutane zasu zaɓa su darje cikin yan takara. Zaka ji suna furuci kan abubuwa amma ba zaka ji suna faɗin hanyar shawo kan matsalolin ba."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Za su yi magana kan yadda Najeriya ta zama koma baya a ɓangaren ilimi, lafiya, tsaro da sauran su amma ba zaka taɓa jin sun yi magana kan hanyoyin shawo kan matsalolin ba da yadda zasu ji da su."
"Yan Najeriya za su saurari kowane ɗan takara amma a wannan lokacin ba wanda zai yarda a yaudare shi."
Abinda ake yaɗawa a kai na ba gaskiya bane - Kachikwu
Ɗan takarar ya musanta zarge-zargen da aka rataya masa cewa ba ya biyan haraji kuma yana da hannu a wani batun cin hanci da rashawa a Amurka, inda ya ce duk kulla-kullar mutanen da ya lallasa a zaɓen fidda gwanin ADC ne.
"Bana son abinda zai ɗauke mun hankali, mutane sun san idan ka fito yi wa al'umma aiki dole wasu su rinka sukar ka. Suka ba wani abu bane, amma su san me suke yi."
"Mun maida hankalin kan kanfen yadda zamu shiga Aso Villa shekara mai zuwa. Ba zamu tsaya wasu tsiraru sun kashe mana kwarin guiwa ba."
A wani labarin kuma Gwamnan arewa ya faɗi manyan dalilai uku da suka sa baya iya biyan ma'aikata Albashi a jiharsa
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce ya zama abu mai wahala biyan ma'aikatan jihar Albashi.
Rahoto ya nuna cewa ma'aikatan jihar sun jima suna koka wa kan rashin biyansu Albashi tsawon watanni uku kenan.
Asali: Legit.ng