Zaben 2023: Shahararren 'Dan kasuwan Najeriya ya ba takarar Peter Obi kwarin gwiwa
- Obinna Obi Iyiegbu watau 'Obi Cubana' ya shiga cikin jirgin magoya bayan Peter Obi a zaben 2023
- Attajirin ya tallata ‘Dan takaran na LP a shafinsa na Twitter, yake cewa shi ya fi dacewa da mulki
- Cubana ya sha alwashin taimakawa tsohon Gwamnan Anambran wajen ganin ya kai labari a 2023
Shugaban kamfanin Cubana Group, Obinna Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana, ya shiga sahun taurarin da suka yi magana kan harkar siyasa.
Daily Trust a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni 2022, ta rahoto Obi Cubana yana mai nuna goyon bayansa ga ‘dan takarar nan na LP watau Peter Obi.
Da yake bayani a shafinsa na Twitter, Attajirin ya nuna cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ne kadai wanda zai iya ceto al’ummar kasar nan.
Cubana mai shekara 47 a Duniya ya bugi kirji yana cewa Obi zai samu galaba a zabe mai zuwa.
Kafin ‘dan kasuwan ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga tafiyar Obedient, mawakin nan Peter Okoye MrP ya dade yana tallata takarar ‘dan siyasar.
“Peter Obi ne kadai zabin da ya rage domin gyara Najeriya. Mun shirya, kuma za mu bada gudumuwa. Zai yi nasara a zaben 2023.” - Obi Cubana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan maganar da ya yi a Twitter, mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu; Wasu sun yarda da abin da Cubana ya fada, wasu kuma sun nuna adawarsu.
The Nigerian Voice ta kawo rahoton @chimnosy2 tana cewa su na tare da Obi Cubana, kuma ana bukatar a wayar da kan sauran al’umma da ke kauyuka.
“Mu na bukatar wayar da kan mutanen karkara a kan Peter Obi da LP. Sun dade su na zaben wasu jam’iyyun, sai mu cusa masu LP tun wuri.” - @chimnosy2.
“A fada da babbar murya, ya kamata kowa ya ji wannan.” - @moses adeyem.
Obi zai yaki APC da PDP
Peter Obi yana cikin wadanda suke tada kura a masu neman kujerar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa. ‘Dan siyasar ya tsaya takara ne a jam’iyyar LP.
Obi ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar LP ta ‘yan kwadago ne bayan ya fice daga PDP a lokacin da ake shirin tsaida ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
NNPP ta samu tasgaro
Ku na da labari cewa bayan an bada sanarwar magoya bayan APC da Ibrahim Shekarau sun shiga NNPP a jihar Kano, wasunsu su na neman dawowa da baya.
A garin Bichi ne wasu mutanen Ibrahim Shekarau su ka bada sanarwar sun bar Sardauna a jam’iyya mai kayan dadi, sun ce sam ba za su rabu da APC ba.
Asali: Legit.ng