Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt
- Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa, ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin manyan yan siyasa
- Hotunan Peter Obi yayin da ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike sun haddasa cece-kuce a bangaren siyasar kasar
- Ana ta rade-radin cewa Wike ya fusata kan hukuncin da Atiku Abubakar ya yanke na kin daukarsa a matsayin abokin takararsa gabannin zaben mai zuwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rivers - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya ziyarci gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a Port Harcourt a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni.
Legit.ng ta tattaro cewa sun shafe tsawon awanni suna saka labule a tsakaninsu a gidan Gwamna Wike da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.
Ana dai ta rade-radin cewa Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP bayan ya fadi a zaben fidda gwanin jam’iyyar sannan kuma aka ki zabarsa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, wanda zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.
Tuni hotunan ganawar tasu suka karade shafukan soshiyal midiya musamman ma a kan Twitter.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haduwar manyan yan siyasar biyu ya haddasa cece kuce kasancewar yanzu ba a ga maciji tsakanin Wike da wasu mambobin jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Zuwa yanzu dai babu tabbacin kan abun da suka tattauna amma ba zai rasa nasaba da siyasar 2023 ba.
Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt
A wani labarin, kakakin kungiyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Mista Major Agni, ya bayyana cewa sharadi guda na yin maja tsakaninsu da Labour Party (LP) shine cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi ya yarda ya zama abokin takarar Rabiu Musa Kwankwaso.
Da yake jawabi a talbijin din Arise a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, kakakin na NNPP ya bayyana cewa Kwankwaso ne ya yi nasara cikin yan takarar shugaban kasa 18 a zaben da suka yi kuma har yanzu shine suka fi so ya zama shugaban kasar Najeriya.
Ya bayyana cewa Kwankwaso ya sauya rayukan talakawa, yana mai cewa akwai bukatar a barshi ya jagoranci yarjejeniyar LP/NNPP, jaridar Thisday ta rahoto.
Asali: Legit.ng