Gwamnan Edo ya yarda PDP da APC na fuskantar barazana daga Magoya bayan Peter Obi
- Gwamna Godwin Obaseki yana ganin zaben jihar Ekiti ya nuna inda siyasar Najeriya ta sa a gaba
- Godwin Obaseki yace zuwan PDP na uku a zaben da aka yi kwanan nan ya na nufin akwai matsala
- Mai girma Gwamnan na Ekiti ya nuna magoyan Peter Obi za su iya kawowa APC da PDP cikas a 2023
Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Ekiti, ya fito ya yi wata magana da ake ganin za ta iya kashewa jam’iyyarsa ta PDP mai adawa kwarin gwiwa.
A ranar Talata, 21 ga watan Yuni 2022, Daily Trust ta rahoto Mai girma Godwin Obaseki yana mai cewa al’umma sun gaji da APC da kuma jam’iyyarsu ta PDP.
Wani gajeren bidiyo da ya bayyana, ya nuna Obaseki yana cewa mutane sun fara neman wata mafita dabam da APC da PDP da suke rike da gwamnatoci.
Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana haka ne da aka yi wata hira ta musamman da shi a gidan talabijin na AIT a kan zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi.
Zaben jihar Ekiti
A cewar Gwamnan, zaben sabon gwamnan da aka gudanar a makon da ya gabata, ya tabbatar da cewa siyasar kasar nan ta na canzawa daga yadda aka sani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dele Momodu ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Instagram, inda aka ji Gwamnan ya na mai kokawa a kan yadda PDP ta sha kashi a zaben na jihar Ekiti.
“Me zai hana PDP, a ce jam’iyyar PDP ba ta ci zabe ba? Ba su ma zo na biyu ba. Saboda za ku iya ganin an dauki wani sabon salo, kuma ba mu son haka.”
“Makomar siyasar kasar mu ta na canzawa.”
“Ban sani ba ko kuna lura da abubuwan da ke faruwa; yanayin rashin jituwa a jam’iyyun. Na tabbata yanzu a gidajenku akwai masu kiran kansu ‘Obidients’.
“Ban sani ba ko ku na da wadannan mutanen a gidajenku. Amma ku tambaye su (’Yan Obidients) ko su ‘yan wani jam’iyya ne; za ku fahimci ba su son mu."
“Ba maganar PDP ko APC suke yi ba. Su na neman wata mafitar ne, kuma su na da yawa.”
- Godwin Obaseki
An ji Obaseki a rahoton yana cewa ya zama dole PDP ta yi kokarin tallata jam’iyyar da kyau, idan ba haka ba kuwa, za ta iya shan mamaki a zaben 2023 mai zuwa.
NNPP a Kano
A jiya kun ji labari bayan an bada sanarwar magoya bayan APC da Ibrahim Shekarau sun shiga NNPP a jihar Kano, wasunsu sun fara dawowa da baya yanzu.
Wasu mutanen Ibrahim Shekarau sun bar Sardaunan Kano a jam’iyya mai kayan dadi, sun ce sam ba za su rabu da Gwamnatin Ganduje a zaben da za ayi a 2023 ba.
Asali: Legit.ng