Wani Dan Sakkwato ya ce ana masa barazanar kisa da matarsa saboda yana goyon bayan Obi ya gaji Buhari a 2023

Wani Dan Sakkwato ya ce ana masa barazanar kisa da matarsa saboda yana goyon bayan Obi ya gaji Buhari a 2023

  • Wani mutumin jihar Sakkwato ya koka cewa ana yi masa barazanar kisa saboda kawai yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi
  • Mutumin mai suna Jamilu Sufi ya ce har ta kai wanda ke razana shi ya kira matarsa yana yi mata barazana itama cewa zai kashe ta idan bata hakura da tallata Obi ba
  • Sai dai wanda ake zargin ya karyata batun inda ya ce kwata-kwata ma shi baya hulda da masu goyon bayan Obi don shi dan APC ne

Sokoto - Wani dan jihar Sakkwato mai suna Jamilu Sufi, ya yi ikirarin samun barazanar mutuwa saboda yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu

Mista Sufi ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Mista Obi, ya kasance dan jihar Anambra daga yankin kudu maso gabas.

Peter Obi
Wani Dan Sakkwato ya ce ana masa barazanar kisa da matarsa saboda yana goyon bayan Obi ya gaji Buhari a 2023 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sufi ya ce mutumin da ke masa barazana ya kuma kira matarsa sannan ya yi barazanar kasheta itama idan har shi (Sufi) ya ki janyewa daga goyon bayan Obi da yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sufi ya ce:

“Ba zan saduda ba saboda cin zarafi ko barazana.”

Ya kuma saka lambar waya mallakar mutumin da ya zarga da yi masa barazana.

Ya ci gaba da cewa:

“Ya kai inda ya kira matata sannan ya yi barazanar kashe ta itama. Na toshe lambarsa amma shi da sauran gayu suna ci gaba da yi mun da matata barzana.”

Kara karanta wannan

Ba dai a 2023 ba: Babangida Aliyu ya sha Peter Obi, ya ce ba zai yi mulki ba sai 2027 ko 2031

Mista Sufi ya ce mutumin na magana da harshen Igbo da Hausa tiryan-tiryan. Ya ce mutumin ya kuma aika masa da sakon murya ta WhatsAPP sannan ya yi barazanar kashe shi.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Sufi ya fada mata ya kai batun ofishin yan sanda a jihar Sakkwato.

Sufi dai ya dade yana amfani da Twitter wajen tallata Obi a jihar Sakkwato da arewa maso yamma.

Wanda yake zargin ya karyata batun yi masa barazana da mutuwa

Jaridar Premium Times ta ce ta tuntubi mutumin da wayarsa da Sufi ya wallafa amma sai ya karyata batun yi masa barazana.

Ya bayyana kansa a matsayin Buhari, amma ya yi ikirarin cewa shi dan kabilar Igbo ne, amma dai ya musulunta a jihar Kano.

Ya ce:

“Ba gaskiya bane. Ku yi watsi da batun kwata-kwata sai dai idan kuna da hujjar nuna mani.”

Da aka tambaye shi kan ko ya taba yiwa Sufi barazana sai ya ce:

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

“Ban ma san wani mai sunan ba. Bana hulda kwata-kwata da mutanen Peter Obi. Ni dan jam’iyyar All Progressive Congress ne. suna na ba Kingsley ba. Sunana Buhari.”

Ba dai a 2023 ba: Babangida Aliyu ya sha Peter Obi, ya ce ba zai yi mulki ba sai 2027 ko 2031

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya bayyana cewa ba lallai ne yan Najeriya sun shirya zabar Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba a 2023.

Aliyu wanda ya kasance babban jigo na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne a wata hira da gidal talbijin na Channels.

Ya kuma bayyana cewa mutane da dama a jam’iyyar PDP na ta kamun kafa don Obi ya zama mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng