Ba zan yarda ba, Nuhu Ribadu ya shigar da kara kotu kan zaben fidda gwanin gwamnan Adamawa

Ba zan yarda ba, Nuhu Ribadu ya shigar da kara kotu kan zaben fidda gwanin gwamnan Adamawa

  • Da alamun jam'iyyar APC za tayi biyu babu a jihar Adamawa yayinda Nuhu Ribadu ya shigar da jam'iyyar kotu
  • Ribadu ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben fidda gwanin ba saboda an tafka magudi
  • Sanata Aishatu Binani ta lallasa Nuhu Ribadu da sauran yan takara biyar a zaben fidda gwanin jihar Adamawa

Tsohon Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Nuhu Ribadu, ya shigar da kara kotu kan zaben fidda gwanin gwamnan Adamawa karkashin jam'iyyar APC.

Nuhu Ribadu ya bukaci kotu tayi watsi da zaben da Sanata Aishatu Binani ta samu nasara kansa, rahoton Leadership.

Alkalin babban kotun tarayya dake Yola, AbdulAziz Anka, ya ce zai saurarin Nuhu Ribadu ba sai ya sanar da Aisha Binani, cewa ya shigar da ita kara.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Duk da cewa jigogin jam'iyya sun yi yunkurin sulhu tsakanin Ribadu da Binani, abin ya ci tura.

Nuhu RIbadu
Ba zan yarda ba, Nuhu Ribadu ya shigar da kara kotu kan zaben fidda gwanin gwamnan Adamawa
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda ya shigar kara sun hada da jam'iyyar APC, Sanata Aishatu, da hukumar shirya zabe ta INEC.

Ya bukaci kotu ta bada umurin sake zaben saboda an tafka magudi a zaben.

A cewar karar da ya shigar:

"Zaben fidda gwanin da APC ta gudanar da gwamnan jihar Adamawa ranar 27 ga Mayu, 2022, bogi ne saboda adadin wadanda sukayi zabe yafi adadin wadanda aka tantance yawa saboda haka Sanata Aisha ba ta samu kuri'u mafi rinjaye ba."
"Ina bukatar kotun tayi watsi da zaben."

Asali: Legit.ng

Online view pixel