Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shiga Legas a karon farko bayan ya samu takarar shugaban kasa
- ‘Dan takaran na APC ya wanke kan shi daga babatun da aka ji ya yi wajen neman tikitin jam’iyya
- A lokacin, Tinubu ya ce a dalilinsa ne Muhammadu Buhari da Dapo Abiodun suka dare kan mulki
Lagos - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda yake rike da tutar jam’iyyar APC mai mulki ya yi karin haske a kan babatun da aka ji ya yi kwanakin baya.
Daily Trust ta rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni 2022, yana cewa ya yi hakan ne saboda ya lura ana neman yi masa kafa.
Da yake jawabi a fadar Mai martaba Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, an ji Tinubu yana bayanin fito da abin da ya birne na tsawon shekaru a cikin zuciyarsa.
Kamar yadda ya bayyana a ranar Lahadi, ‘dan takaran na APC ya ce an nemi kai shi bango. Hakan ta sa aka ji ya yi wa shugaban kasa da gwamnan Ogun gori.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legas ta samu 'Dan takara
Bola Tinubu yake cewa a tarihin jihar Legas, ba a taba samun wani mutumin jihar da ya zama shugaban kasa ba, sai shi ne yake neman karya wannan tarihi.
Duk da irin gudumuwar da Legas ta ke badawa a tarayya, mafi girman matsayin da jihar ta samu a gwamnatim sama shi ne Alkalin Alkalai na kasa a can baya.
“Na dauki wannan yaki domin kafa tarihi. Yakin neman tikitin jam’iyyar APC ya zo da wahala. A lokacin da na kusa kai bango, sai na komawa addu’a.”
“Sannan kuma na yi aman abin da yake cikin rai na a lokacin da na yi tunanin wasu (a jam’iyyar APC) sun yi mani gayya, an shirya mani taron dangi.”
Na godewa Ubangiji, tun da a karshe nayi nasarar samun takarar shugaban kasan.” - Bola Tinubu.
Aikin da ya ragewa APC
Pulse ta rahoto tsohon gwamnan na Legas yana cewa akwai bukatar a wayar da kan al’umma domin su kada kuri’arsu a zaben shugaban kasa na 2023.
Asiwaju Tinubu ya ce muhimmin abu shi ne a ga yadda mutane za su mallaki katin PVC domin jefa kuri’arsu domin ganin mulki ya fada hannun ‘Dan Legas.
Abokin takarar Tinubu
Abdulazeez Yinka-Oniyangi ya ce yawan kuri’u za a duba wajen fito da abokin takarar Bola Tinubu. A makon jiya ne mu ka fitar maku da wannan rahoto.
Oniyangi ya ce Musulmai ba su da rinjaye a Kudu, don haka dole APC ta dauko Musulmin Arewa ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Asali: Legit.ng