Mambobin APC da PDP a wata mazaɓar Imo sun rushe tsarin su, sun koma bayan Peter Obi
- Yayin da ake ta shirin tunkarar babban zaɓen 2023, a jihar Imo manyan jam'iyyun kasar nan APC da PDP sun shiga babban ruɗani
- Mambobin jam'iyyar APC mai mulki da mai hamayya PDP a shiyyar Imo ta arewa sun rushe tsarin su zuwa LP, sun koma bayan Obi
- A cewarsu shekara 23 kenan APC da PDP ke ƙara dagula Najeriya, lokaci ya yi da Obi zai ceto ƙasar daga rushewa
Imo - Mambobin manyan jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya, APC da PDP, a mazaɓar Sanata mai wakiltar Imo ta arewa sun rushe tsarin su zuwa cikin jam'iyyar Labour Party (LP) ranar Lahadi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa baki ɗayan mambobin mazaɓar sun yi mubaya'a tare da goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi.
Aƙalla mutum 2,000 ne suka koma jam'iyyar LP a wani taro na musamman da aka shirya a ƙauyen Umuaro, ƙaramar hukumar Isiala Mbano, jihar Ribas.
Tsohon mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar lokacin mulkin wani tsohon gwamnan Imo, Chikwem Onuoha, ya ce sun cimma matsayar haka ne bayan wani bincike da suka yi game da yan takara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa binciken ya nuna cewa Obi ya fi sauran yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya cancanta da kwarewar ya gaji shugaba Buhari a 2023.
Onuoha ya ƙara da cewa jam'iyyun PDP da APC sun gurguntar da Najeriya na tsawon shekara 23, inda a ganinsa lokaci ya yi da yan Najeriya zasu kaɗa wa Obi ƙuri'un su don ceto ƙasar nan.
Tsohon Jigon APCn ya ce:
"Daga yau APC da PDP sun mutu murus a shiyyar Okigwe, mun yanke rushe tsarin fasalin mu na shiyyar zuwa cikin jam'iyyar LP kuma zamu yi aiki tuƙuru don nasarar Peter Obi."
"Peter Obi ɗan siyasa ne da aka gwada kuma aka ga amanarsa, yana da goyon bayan mutane waɗan da suka kaɗa kuri'a lokacin zaɓe. Bayan Obi, jam'iyyar LP zamu zaɓa sak, tun daga sama har ƙasa."
Shugaban matasan yankin Okigwe ta arewa, Chidinma Onyenagubo, ya ce tawagarsa sun fara wayar da kan mutane su tabbatar sun yi rijista sun karɓi katin zaɓe don kaɗa wa Obi kuri'un su a 2023.
A wani labarin kuma mun haɗa muku wasu Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti
Ɗan takarar jam'iyyar All Progressive Congress APC, Mista Biodun Oyebanji, ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ekiti wanda ya gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022.
Da yake ayyana wanda ya samu nasara, baturen zaɓe na hukumar INEC, Farfesa Oyebode Adebowale, ya ce Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 da suka ba shi damar zama zakara a zaɓen.
Asali: Legit.ng