Zulum ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki na APC
- Kungiyar masu ruwa da tsaki na APC ta nemi shugabancin jam'iyyar da Shugaba Buhari da su tsayar da Gwamna Babagana Zulum a matsayin abokin takarar Tinubu
- A cewar kungiyar Zulum ne kadai zai iya kawowa jam'iyyar jihohin arewa 19 a babban zaben na 2023 mai zuwa
- Kungiyar ta ce aikin da Zulum ya yi a jihar Borno sun isa a bashi damar yin irinsa a kasar don daidaita lamura
Kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi kira ga shugabancin jam’iyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da su duba yiwuwar tsayar da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasarsu.
Kungiyoyin guda 840, wadanda sune suka hada kungiyar, sun yarda cewa idan aka tsayar da Zulum, hakan zai taimakawa jam’iyyar wajen lashe zaben 2023 mai zuwa kuma zai taimaka a kokarin da ake yi na ceto kasar daga durkushewa, Channels tv ta rahoto.
Shugaban kungiyar na kasa, Abdullahi Aliyu Katsina, yayin da yake jawabi ga shugabannin jihohi bakwai na arewa maso yamma a Katsina, ya yi bayanin cewa Gwamna Zulum wanda shi kadai ne ya siye zukatan yan Najeriya saboda irin shugabancinsa tsawon shekaru uku da suka wuce, zai iya sa mutane su zabi jam’iyyar a shekara mai zuwa.
A cewar Katsina, sadaukarwar da Gwamna Zulum ya yi a jihar Borno ya isa da APC za ta bashi wannan damar yin irinsa a Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar ta nakalto yana cewa:
“Bukatarmu a fili take kuma bai fi daukar Gwamna Zulum na jihar Borno a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasar APC ba.
“Mun fahimci cewa Gwamna Zulum ne kadai zai iya kawo kuri’u daga jihohin arewa 19.
“Don guje ma faduwa a zabe, mutum daya a Najeriya a yau wanda zai iya kawo nasarar da ake bukata ga jam’iyyar shine Gwamna Zulum. Duk mutumin da aka dauka a yau a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, idan ba Zulum ba, ba lallai ne ya kawo nasarar da ake muradi ba.
“Gazawar jam’iyyar na daukar Zulum, na iya sawa a rasa zaben.”
Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari
A wani labarin, Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya taya dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin inuwar Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Biodun Oyebanji, murnar lashe zaben da ya yi.
Shugaban kasar ya kuma taya shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da kwamitin aiki na jam’iyyar murna kan wannan nasara wanda ita ce ta farko a karkashin sabuwar shugabancin jam’iyyar.
Asali: Legit.ng