2023: Bola Tinubu ya gaje babban ofishin yaƙin neman zaben Buhari a Abuja

2023: Bola Tinubu ya gaje babban ofishin yaƙin neman zaben Buhari a Abuja

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki, Bola Tinubu, ya samu ofishin yaƙin neman zaɓe na biyu tun bayan nasararsa
  • An bai wa ɗan takaran ofishin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi amfani da shi yayin Kanfe a zaɓen 2019
  • Bola Tinubu ya samu nasarar zama ɗan takarar APC ne bayan lallasa ministan Sufuri mai murabus, Rotimi Amaechi, da sauran su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda aka bude saboda kanfe a 2019 ya koma hannun ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Punch ta ruwaito cewa an baiwa ɗan takarar ofishin ne kwanaki bayan ya samu nasara a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki.

Shugaba Buhari tare da Tinubu.
2023: Bola Tinubu ya gaje babban ofishin yaƙin neman zaben Buhari a Abuja Hoto: @Buharisallau1
Asali: Facebook

Tinubu ya samu nasara kan tsohon ministan Sufuri Rotimi Amaechi, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da sauran yan takara 12 a babban taron APC na musamman a Eagle Square.

Mamba a majalisar wakilan tarayya kuma shugaban wata ƙungiyar magoya bayan Tinubu, James Falake, shi ne ya sanar da wannan cigaban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Falake, wakilin Tinubu a wurin zaɓen APC, ya bayyana cewa Ofishin yaƙin neman zaben wanda ke tsakiyar birnin Abuja na tattare da duk wasu kayan aiki da suka haɗa Na'urori da sauran su.

Ɗan majalisan ya ƙara da cewa tuni aka canza sunan wurin zuwa 'Hedkwatar Kanfen din Tinubu' yayin da sauran Ofisoshi zasu zama rassa.

Shin wannan ne ofis na farko da aka ba Tinubu?

Tsohon ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Buhari shi ne ofis na biyu da aka bai wa jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kyauta domin kamfe.

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya ba Tinubu gudummuwar ofishin Kamfen da ya tanadar domin yakin neman kujerar shugaban ƙasa.

A wani labarin kuma Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

Kotu ta ɗaure wani mutumi na tsawon wata biyu a gidan Gayaran hali bayan kama shi da laifin yaɗa ƙarya kan COVID19 a Facebook.

Mutumin mai suna, Habibu Rabiu, ya yi wani rubuta inda ya ankarar da mutane cewa rasa rayuka na ƙaruwa a Kogi sanadiyyar zazzaɓi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel