Wani mutumi ya fara tattaki da ƙafa daga Bauchi zuwa Legas don kaunar Tinubu a 2023

Wani mutumi ya fara tattaki da ƙafa daga Bauchi zuwa Legas don kaunar Tinubu a 2023

  • Yayin da gangar siyasa ke cigaba da kaɗawa mutane na kokarin nuna goyon bayan su ga ƴan takara ta hanya daban-daban
  • Wani mai suna Usman Adamu ya isa Kafanchan dake Kaduna, ya taso daga Bauchi zuwa Legas don nuna kaunarsa ga takarar Tinubu
  • Duk da wannan ba shine karo na farko ba Najeriya, Adamu ya ce babu wani ɗan siyasa da ya ɗauki nauyinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Wani mutumin ɗan shekara 51, Usman Adamu, ya fara tafiyar kafa daga jihar Bauchi zuwa jihar Legas domin nuna goyon baya ga takarar Bola Ahmed Tinubu ta shugaban kasa a zaɓen 2023.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Adamu, wanda shi ne Madakin Fawa na kungiyar mahauta ta Najeriya, ya isa garin Kafanchan da ke kudancin Kaduna bayan shafe kwana huɗu ya na tafiya.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu ya gaje Babban Ofishin yaƙin neman zaɓen shugaba Buhari a Abuja

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Wani mutumi ya fara tattaki da ƙafa daga Bauchi zuwa Legas don kaunar Tinubu a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Meyasa ya ƙirƙiri wannan tafiya a ƙafa?

Mutumin ya bayyana cewa ya yanke shawarin shafe tsayin kilo mila 1,079.9 da ke tsakanin Bauchi da Legas domin nuna tsananin goyon bayansa ga Tinubu da kuma jam'iyyarsa ta All Progressive Congress wato APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa zata iya tuna muku cewa Hashim Suleiman ya taɓa irin wannan doguwar tafiya a 2015 daga Legas zuwa Abuja domin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Haka zalika an sake samun wani bawan Allah mai suna Buba Ɗahiru, da ya yi tattaki da kafarsa tun daga Gombe zuwa Abuja bayan nasarar shugaba Buhari.

Bayan haka matasa da dama na irin wannan tafiya daga wani wuri zuwa wani a faɗin Najeriya don nuna soyayyar su ga wani ɗan takara.

Shin yana samun tallafi yayin tafiyar?

Da yaje jawabi ga wakilin jaridar a Kafanchan, Adamu ya ce babu wani ɗan siyasa da ya ɗauki nauyinsa a wannan tafiyar, inda ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

"Ina sha'awar yin komai da kuɗina, duk da cewa na samu tsabar kudi da tallafi daga mutane masu mun fatan Alkairi a kan hanya."

Usman Adamu, wanda ya lashi takobin ba zai hau abin hawa ba, ya ce ya hau ɗan Acaba sau ɗaya don wuce wani wuri bayan an gaya masa rayuwarsa na cikin hatsari idan ya bi hanyar da ƙafa.

A wani labarin kuma Ana gab da zaɓe, Tsohon Kwamishina da wasu jiga-jigan APC makusantan Ministan Buhari sun koma PDP

Yayin da kowace jam'iyya ke shirin tunkarar zaɓen gwamnan Osun a wata mai kamawa, APC ta rasa wasu manyan jigoginta.

Tsohon kwamishina da wasu mambobin APC magoya bayan Rauf Aregbesola, ministan cikin gida sun sauya sheƙa zuwa PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel