Manyan dalilai 3 da suka sanya APC ta lashe zaben gwamnan Ekiti

Manyan dalilai 3 da suka sanya APC ta lashe zaben gwamnan Ekiti

A karshe hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Biodun Oyebanji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Ekiti na 2022.

Oyebanji ya samu jimlar kuri’u 187,057 wajen kayar da manyan abokan takararsa – Segun Oni na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bisi Kolawole na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Jam’iyyar SDP ce ta zo ta biyu da jimilar kuri’u 82,211 yayin da PDP ta zo ta uku da kuri’u 67,457.

Zababben gwamnan jihar Ekiti
Manyan dalilai 3 da suka sanya APC ta lashe zaben gwamnan Ekiti Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Sai dai kuma, ba lallai ne wannan nasarar ta yiwu ba idan ba saboda wasu dalilai ba. An gano dalilan kamar haka.

1. Bayyanar jam’iyyar SDP daga PDP

Daya daga cikin manyan galabar da APC mai mulki ta samu shine ballewar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki. Bayan tsohon gwamna Fayose ya dage dan takararsa ne zai daga tutar jam’iyyar, wani tsohon gwamnan jihar, Segun Oni ya bar jam’iyyar don cimma kudirinsa a karkashin inuwar SDP.

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Rawar ganin Fayemi

Kasancewarsa gwamna mai ci, Fayemi ya taka rawar gani wajen nasarar da jam’iyyar APC ta samu a wannan zabe. Baya ga cewar Oyebanji ya kasance dan takararsa, Fayemi yana da damar yin duk mai yiwuwa don ganin ya samu nasara.

3. Yawan siyan kuri’u

Wani abun da ya kai ga nasarar shine siyan kuri’u. An zuba makudan kudi sosai a zaben gwamnan da aka kammala. Wakilan jam’iyya sun tsunduma siyan kuri’u a dili-dili. Jam’iyyar mai mulki na daga daga cikin manyan shugabannin siyan kuri’u. Wannan ya taimaka mata wajen yin nasara.

Jam'iyyar APC ta Lashe Zaben Gwamnan Ekiti, Ta Lallasa Sauran Jam'iyyu a LGAs 15 Daga Cikin 16

Mun kawo cewa Biodun Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, ya tabbata wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Bayan ya bar APC, Adamu Aliero ya lashe tikitin PDP na Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya

Kayode Oyebode, baturen zaben da aka yi a ranar Asabar, ya sanar da sakamakon zaben a sa'o'in farko na ranar Lahadi.

Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 inda ya lallasa manyan masu kalubalantarsa, Segun Oni na jam'iyyar SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 67,457.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng