Lawan ya tsallake rijiya da baya, sunansa ya maye gurbin na Machina a matsayin dan takarar sanata na APC
- Rahotanni sun kawo cewa an bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC na Sanata mai wakiltan Yobe ta arewa
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janye masa ba
- An dai gano sunan Ahmad ne a jerin sunayen yan takarar sanata na jam'iyyar mai mulki wanda aka sanyawa hannu
Yobe - An bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.
Lamarin na zuwa ne yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba.
Lawan dai ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.
Sai dai kuma, manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun yi watsi da shawarar maslahan sannan a karshe Bola Ahmed Tinubu ya lashe tikitin a zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, Machina ya jadadda cewa ba zai janye daga tseren kujerar sanatan ba tunda shi ya samu kuri’un deliget a zaben ba tare da hamayya ba.
Machina ya ce:
“Ina da tabbacin bai yi shirin komawa majalisar dokokin tarayya ba. Wannan ne dalilin da yasa ya nemi takarar shugaban kasa sannan ya fadi. Wannan damokradiyya ne. Filin akwai yanci. An baiwa mutanen da ke son takara wani lokaci. Jam’iyyar ta fitar da jadawali, kuma an gudanar da zabe.”
Sai dai kuma a cikin wata takarda dauke da jerin sunayen yan takara da aka fitar a ranar Juma, an ambaci Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar na Yobe ta arewa, jaridar The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng