Yan Sanda Sun Nemi A Biya Su 'Allawus Na Siyan Kororon Roba' Yayin Da Suke Waka Da Rawa Gabanin Zaben Ekiti
- Wasu jami'an yan sanda da aka tura jihar Ekiti domin zaben gwamna na 2022 sun nuna alamun cewa a shirye suke su kare masu zabe
- An kuma hangi yan sandan suna rawa da wakoki yayin da suke atisayensu na nuna shirinsu na kare mutane yayin zaben
- Yayin atisayen, jami'an tsaron sun kuma nemi a basu kudaden allawus da za su siya kororon roba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya wanda aka tura su samar da tsaro a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar 18 ga watan Yuni a Jihar Ekiti sun gabatar da babban bukata.
Jami'an yan sandan yayin atisayen da suka yi na nuna shirinsu a hedkwatar rundunar yan sanda na Jihar Ekiti a Ado Ekiti sun nemi a basu allawus na siyan kororon roba, rahoton Legit.ng.
Kuma domin nuna cewa sun shirya tsaf domin kare rayuka da dukiyoyin a zaben gwamna na shekarar 2022 wanda za a yi kasa da awa 24, an hangi jami'an yan sandan suna rawa da wakoki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A yayin da suke rera wakoki daban-daban masu ban dariya, daya daga cikinsu ya bukaci a biya su allawus dinsu na kororon roba yayin bada amsa cikin nishadi.
An kuma hangi jirgi mai saukan ungulu da aka samar a jihar domin taimakawa yan sandan yana yawo kasa-kasa a sararin samaniya a babban birnin jihar.
Yan sandan wadanda suka fito daga sassa daban-daban na rundunar suna ta gudanar da harkokinsu cikin annashuwa yayin atisayen.
Zaben Gwamnan Ekiti: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba
A wani rahoton, gabanin zaben gwamnan Jihar Ekiti, mazauna jihar wadanda suka yi magana da Legit.ng sun bayyana yan takarar da suka fi so a cikin wadanda ke neman kujerar gwamnan jihar.
Akwai yan takarar gwamna guda 16 da suka shiga takarar na neman gaje kujerar Gwamna Kayode Fayemi.
Wasu cikin yan takarar su ne: Oluwole Oluyede na African Democratic Congress (ADC); Kemi Elebute Halle na Action Democratic Party (ADP); Biodun Oyebanji na All Progressives Congress (APC); Olabisi Kolawole na Peoples Democratic Party (PDP); tsohon gwamna Segun Oni, na Social Democratic Party (SDP) da Ranti Ajayi daga Young Progressives Party (YPP).
Asali: Legit.ng