Kwankwaso: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba

Kwankwaso: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba

  • Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP ya ce yana da tabbas jam'iyyarsa za ta ci zabe a 2023
  • Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce ba zai janye wa kowa takara ba domin jam'iyyarsu ta samu karbuwa a wurin mutane a dukkan sassan Najeriya
  • Kwankwaso ya ce baya ganin yan takarar manyan jam'iyyun APC da PDP a matsayin kallubale domin ba shine zai kada su ba, mutane masu zabe za su kada su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce ba zai janye wa kowa takararsa ba har da yan takarar manyan jam'iyyun APC da PDP, wato Bola Tinubu da Atiku Abubakar.

Jagoran na Kwankwasiyya ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da ya yi da wakilin Jaridar The Punch, Abiodun Sanusi.

Kara karanta wannan

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

Rabiu Musa Kwankwaso.
2023: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba, Kwankwaso. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce tafiyar Kwankwasiya ta bazu dukkan sassan Najeriya kuma ya yi farin cikin ganin an ratabba hannu kan sabuwar dokar zabe don hakan na nufin zai yi wuya a murde zabe kamar yadda aka saba yi a baya.

"Muddin za a yi zabe na adalci, zai yi wahala wani ya doke mu, ina da tabbacin samun nasara kan dan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu da na PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023," in ji Kwankwaso.

Yayin da ya ke amsa tambaya kan yiwuwar janye wa Atiku a zaben don kayar da APC, ya ce:

"Ba zan janye wa kowa ba, jam'iyyar mu ta yi fice a dukkan sassan kasar nan, muna da tabbacin za mu ci zabe.
"Mun zabi yan takarar mu ne kan cancanta da aiki. Yan Najeriya ba za su zabi wani don gwaji ba yanzu, mutane na neman wadanda suka yi aiki a baya. Yan Najeriya na neman wanda zai hada kan al'umma, inganta ilimi, kawo karshen rashin tsaro. Mun dade muna kulawa da al'umma, musamman talakawa, mun yi farin ciki da na samu tikitin takarar shugaban kasa na NNPP."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku ya shiga ganawa da Gwamnonin PDP kan zabo abokin takararsa

Kwankwaso ya ce baya ganin Tinubu da Atiku a matsayin kalubale domin ba shi ne zai kada su ba, talakawan Najeriya ne za su kada su saboda sun yarda da jam'iyyar NNPP.

"Duk da suna na da tambarin jam'iyyar mu ne ke takardar zabe, mutane ne za su fita su kada kuri'a su kayar da su domin sun san banbanci tsakanin ni da sauran yan takarar manyan jam'iyyun, yan Najeriya sun san su, sun san babu wani sabon abu da za su musu, kuma mutanen sun san abin da na yi imani da shi," in ji shi.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Kara karanta wannan

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164