Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

A yau ne dan takarar shugaban kasa a PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana wanda zai tsaya a matsayin mataimakinsa a zaben 2023 mai zuwa.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ne Atiku ya darje ya zaba, daidai lokacin da wa'adin da INEC ta dibarwa jam'iyyu na bayyana 'yan takararsu ke gab da karewa.

Waye Okowa? Wannan ita ce tambayar da mutane ka iya neman sanin amsarta. Legit.ng Hausa ta yi duba ga rayuwarsa da kuma gwagwarmayar siyasarsa domin sanin waye shi.

Abinda ya kamata ku sani game Ifeanyi Okowa
Okowa: Abubuwa 3 da ya kamata a sani game da abokin takarar Atiku a PDP | Hoto: ngnews247.com
Asali: UGC

Rayuwarsa da karatunsa

1. Ifeanyi Arthur Okowa, an haife shi a ranar 8 ga Yulin 1959 a Owa-Alero ta karamar hukumar Ika ta Arewa a jihar Delta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

2. Ya yi karatu a kwalejin Edo a birnin Benin, ya kuma zarce zuwa jami'ar Ibadan, inda ya karanta likitanci, inji wata makalar jaridar Vanguard.

3. Kasanncewarsa kwararren likata mai lasisi ya kuma kammala karatunsa na digirin likitanci yana da shekaru 22, ya yi ayyuka da suka shafi likitanci kafin ya shiga siyasa.

Tafiyar siyasa

4. Bayan rike kananan mukamai na siyasa a jihar ta Delta, Okowa ya shiga jam'iyyar PDP tun farko-farkonta a shekarar 1998.

5. Ya yi aiki a matsayin kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Delta (Yuli 1999 – Afrilu 2001), Raya albarkatun ruwa (Afrilu 2001 – Mayu 2003) da lafiya (Satumba 2003 – Oktoba 2006).

6. A shekarar 2007, Okowa ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan lafiya a yunkurinsa na zama gwamnan jihar. Sai dai kash, ya sha kaye a zaben fidda gwani na gwamnonin PDP. Sai dai an biya shi diyya tare da nada shi a matsayin sakataren gwamnatin jihar Delta.

Kara karanta wannan

2023: Ba A Ga Wike Ba A Wurin Taron Gabatar Da Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku

7. A shekarar 2011, ya tsaya takarar kujerar Sanata a yankin Delta ta Arewa, inda ya samu nasara.

8. A matsayinsa na dan majalisar dattawa a majalisa ta bakwai, ya kasance cikin sanatoci da suka fi daukar nauyin kudirori.

Ya gabatar da kudurori akalla guda 10 da suka hada da kudirin dokar kiwon lafiya ta kasa, abin da mutane da yawa suka yarda da shi a matsayin hazaka, bajinta da abin yabawa duk da cewa ya dan jawo cece-kuce a zauren majalisar.

9 . An rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayun 2015 bayan lashe zaben jihar da aka gudanar a watan Afrilun 2015, rahoton Premium Times.

Ya sake lashe zaben gwamna a ranar 29 ga Mayu, 2019, kamar yadda a baya Vanguard ta ruwaito.

10 A yau dinnan, ranar 16 ga watan Yuni, 2022 Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya zabe shi a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

Zargin rashawa

11. A mulkinsa na farko, an kai ruwa rana kan batun mayar da sufurin Delta Line zuwa kasuwanci mai zaman kansa.

An rahoto cewa, an sayar da Delta Line ga wani kamfani mai suna God is Good Transport Development Company (GTDC) da ake zargin na da alaka da gwamnan da yakin neman zabensa, lamarin ya jawo bincike mai zurfi da sharhin kwararru, kamar yadda ICIR ta tattaro.

12. A wani zargin, a Disamba 2021, wani bincike kashi biyu na Cibiyar Bincike ta Duniya ta gano kashe-kashen kudade ba bisa ka'ida ba, rashin mutunta ka'idojin kudi, da kuma alamun almubazzaranci a cikin rahoton shekara-shekara na Odita-Janar na Jihar Delta na 2019.

Ma’aikatu da hukumomi da dama tare da majalisar dokokin jihar ne aka dorawa alhakin rashin bin ka’ida wajen binciken rahoton.

Rahoton cibiyar ya bibiyi diddigin kudaden da ke kai, inda ya ba da cikakken bayani na inda ake kyautata zaton sun yi batan dabo.

Kara karanta wannan

2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP

Shirin 2023: PDP ta yi watsi da batun zaban Wike a matsayin abokin takarar Atiku

A wani labarin, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da rade-radin da ake yi cewa kwamitinta ya zabi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.

Vanguard ta ruwaito cewa, kwamitin zaben na jam’iyyar PDP, ya yi taro a jiya, domin cika aikin da ya rataya a wuyansa na ba da shawarar kan abokin tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.

Da yake magana kan wannan lamari a Abuja, Laraba, Sakataren Yada Labarai na kasa na PDP, Debo Ologunagba, ya ce rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa PDP ta zabi Wike kawai jita-jita ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.