Abokin takarar Tinubu: Kungiyar APC ta tsayar da gwamnan Neja, Sani Bello

Abokin takarar Tinubu: Kungiyar APC ta tsayar da gwamnan Neja, Sani Bello

  • Wa’adin da hukumar zabe ta dibarwa jam’iyyun siyasa domin su fitar da yan takararsu na mataimakin shugaban kasa na kara gabatowa
  • Ana ci gaba da baiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, shawarwari kan wanda ya kamata ya zaba a matsayin abokin takararsa
  • Wata kungiyar APC ta bukaci jam’iyyar da Tinubu da su zabi gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, cewa ya dace da wannan kujerar

Abuja - Wata kungiyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin inuwar APC Patriots (APC-P) ta yi kira ga shugabancin jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da su duba sannan su zabi gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: PDP ta yi watsi da batun zaban Wike a matsayin abokin takarar Atiku

Yayin da jam’iyyar ke da kasa da makonni biyu don yanke shawara kan wanda zai daga tutarta na mataimakin shugaban kasa, an yi ta samun ra’ayoyi mabambanta game da abubuwan da ya kamata a duba wajen tsayar da wanda zai dare kujerar.

Gwamna Sani-Bello tare da Bola Tinubu
Abokin takarar Tinubu: Kungiyar APC ta tsayar da gwamnan Neja, Sani Bello Hoto: Niger state government
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a cikin wata sanarwa da shugaba da sakataren kungiyar, Prince Zadok Bukar da Cif Omini Ofem suka saki a ranar Laraba a Abuja, sun ce:

“Kiran da aka yi na a tsayar da gwamna Sani Bello a matsayin mataimakin Tinubu ya kasance ne saboda kokarinsa a matsayin gwamna, karbuwarsa a tsakanin takwarorinsa da yan Najeriya, adalcinsa da daidaito da kuma gudunmawarsa wajen ci gaban APC a matsayinta na jam’iyya mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamna Sani Bello ya yi fice saboda halayensa na kirki da kuma tausasawarsa.
Ya kasance gada tsakanin matasa da tsofaffi, kuma bai da tarihi na zafafa lamuran addini. Ya kasance mutum mai ji da karfin jiki da na hankali kuma mai dinke baraka tsakanin arewa da kudu da sauransu.

Kara karanta wannan

Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Yafi Dace Wa Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023

“Kwarewar da ya samu a wajen shugabancin jihar Neja ko shakka babu zai yi amfani a rawar da zai taka a matsayin mataimakin shugaban kasa.
“Idan ana maganar gogewar aiki, Sani Bello, wanda ya yi gwamna sau biyu yana da masaniya kan yadda ake gudanar da mulki, kasancewarsa gwamnan jiha mafi girma a kasar nan.
“Mun yi amanna cewa duk mutumin da zai iya shugabancin jihar Neja cikin nasara kamar yadda Gwamna Sani Bello ya yi ya cancanci samun mukamin mataimakin shugaban kasa.”

Da take tuna gudunmawar da Sani-Bello ya baiwa jam’iyyar, kungiyar ta ce:

“Baya ga kasancewarsa dan jam’iyya mai biyayya, bai kamata shugabanni da mambobin jam’iyyar su manta yadda gwamnan na jihar Neja ya gaggauta ceto APC a lokacin da ta ke gab da kifewa kafin bayyanar kwamitin aiki da Sanata Abdullahi Adamu ke jagoranta, da sauran gudunmawar da ya bayar."

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

Kara karanta wannan

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress(APC) mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin daukar dan uwansa Musulmi a matsayin abokin takara.

Tinubu ya yi jawabin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a yayin gangamin APC da aka gudanar a jiya Talata a Ekiti gabannin zaben gwamnan jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Sai dai kuma, ya nesanta kansa daga jita-jitan, yana mai cewa wadanda suke yada ta basa bisa tsarin dimokradiyya kuma sun tsorata ne da nasarar da zai samu a babban zaben shugaban kasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng