Sanatan Oyo ya yi murabus daga jam'iyyar PDP, ya koma APC a hukumance

Sanatan Oyo ya yi murabus daga jam'iyyar PDP, ya koma APC a hukumance

  • Sanata mai wakiltar kudancin jihar Oyo, Sanata Kola Balogun, ya tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance
  • Sanatan ya aike da wasikar matakin da ya ɗauka ga shugaban majalisar dattawa kuma ya karanta a zaman su na ranar Laraba
  • A cikin wasikar, Balogun ya bayyana dalilansa na tattara kayansa da barin PDP tare da magoya bayansa baki ɗaya

Oyo - Sanata Kola Balogun mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a hukumance kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Matakin Sanatan na kunshe ne a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, kuma ya karanta a zaman majalisar na yau Laraba.

Kara karanta wannan

Sauya sheƙa: Shugabannin majalisar dattawa biyu sun yi murabus daga kujerunsu a hukumance

Sauya Sheƙarsa ya kara yawan Sanatocin jam'iyyar APC mai mulki zuwa 70 a majalisar Dattawan tarayyan Najeriya.

Sanata Kola Balogun.
Sanatan Oyo ya yi murabus daga jam'iyyar PDP, ya koma APC a hukumance Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Meyasa ya sauya sheka zuwa APC?

Ya ce ya ɗauki matakin barin PDP ne saboda rashin adalci da demokariɗiyyar cikin gida a reshen jihar Oyo wajen zaɓen shugabanni da wakilai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanatan ya ƙara da cewa hakan ya jawo jam'iyyar ta dare zuwa tsagi daban-daban kuma ya jawo fanɗarewar wasu tawagar mambobin cikin gida.

Punch ta ruwaito Wani sashin wasiƙar Sanata Balogun ya ce:

"Na ɗauki matakin Murabus ne saboda samun wurin gwamna da ya haddasa wuce gona da iri da kwace haƙƙin masu ruwa da tsaki na jam'iyya tare da maye gurbin su da wasu mutane daban."
"Wannan saɓa wa abin da kundin mulki ya tanada ne wajen zaɓen shugabanni da wakilan al'umma kuma ba bu tantama shi ne musabbabin darewar jam'iyya da fusata wasu mambobi da masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyya bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

"Na rubuta wannan wasiƙa ne domin sanar da mambobin majalisar dattawa cigaban da PDP ta samu a jihar Oyo da kuma inda ni da mutane na muka dosa yanzu."

A wani labarin kuma Gwamna Zulum ya naɗa sabbin kwamishinoni 20, ya tura sunayen su ga Majalisar Borno

Gwamna Babagana Umaru Zulum ya gabatar wa majalisar dokokin Borno sunayen mutum 20 da zai naɗa kwamishinoni.

Zulum ya sallami mambobin kwamitin zartarwan jihar ne a watan da ya gabata yayin da APC ta fara gudanar da zaɓen fidda yan takara na zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel