Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya magantu kan rade-radin zai dauki abokin takara Musulmi
- Da yake martani, Tinubu ya ce wadanda ke bakin ciki da nasarar da zai samu a zaben 2023 ne ke yada wannan jita-jitan
- Ya bayyana cewa babu mai tursasa masa daukar wani inda ya ce abokin takararsa zai fito ne daga yankin arewa maso gabashin kasar
Ekiti - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress(APC) mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin daukar dan uwansa Musulmi a matsayin abokin takara.
Tinubu ya yi jawabin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a yayin gangamin APC da aka gudanar a jiya Talata a Ekiti gabannin zaben gwamnan jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Sai dai kuma, ya nesanta kansa daga jita-jitan, yana mai cewa wadanda suke yada ta basa bisa tsarin dimokradiyya kuma sun tsorata ne da nasarar da zai samu a babban zaben shugaban kasa mai zuwa.
Da yan jarida suka tambaye shi game da zabinsa na mataimakin shugaban kasa, sai Tinubu ya jadadda cewa tikitin mataimakin shugaban kasa na yankin arewa masu gabas ne kuma ma kiristoci, koda dai ana kan tattaunawa kan wanda za a tsayar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Tikitin mataimakin shugaban kasar na yankin arewa maso gabas ne kuma ma kiristoci, amma ana kan tattaunawa kan wanda za a yanke hukuncin tsayarwa.”
Tinubu ya ba yan Najeriya tabbacin cewa babu kungiya ko wani mutum da zai iya tursasa mataimakin shugaban kasa a kansa. Ya bayyana cewa zai zabi mataimakin shugaban kasa da kansa kuma wanda zai amfani yan Najeriya, jaridar Independent ta rahoto.
Tun farko dai Tinubu ya yi watsi da batun tikitin Musulmi da Musulmi tun ma kafin a zabe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Da yake zantawa da manema labarai a jihar Ekiti, wani mamba na kungiyar kamfen din Tinubu, Comrade Bolaji Tosin ya kuma bayyana cewa hadin kai, zaman lafiya da aiki shine babban abun da gwamnatin Tinubu za ta baiwa fifiko.
Musulmi da Musulmi: Yan Najeriya basu damu da addinin yan takara ba – Baba Ahmed
A gefe guda, kakakin kungiyar dattawan arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa a yanzu talakawan Najeriya basu damu da addinin shugabannin siyasarsu ba.
Daily Trust ta rahoto cewa Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 14 ga watan Yuni, yayin wata hira da gidan talbijin na Channels.
A yan kwanakin nan, ana ta cece-kuce a kasar kan addinin yan takarar shugaban kasa da kuma wadanda za su tsayar a matsayin abokan takararsu.
Asali: Legit.ng