Tashin hankali: Rikici ya barke yayin da aka kashe wani jigon jam'iyyar APC

Tashin hankali: Rikici ya barke yayin da aka kashe wani jigon jam'iyyar APC

  • An samu tashin-tashina a wani yankin jihar Ekiti yayin da 'yan bangan siyasa ke yawon kamfen a jihar
  • An ruwaito cewa, an hallaka wani dan jam'iyyar APC, inda ake tunanin samun martani daga bangaren
  • Rahoton da muka samo daga majiyoyi sun bayyana cewa, rundunar 'yan sanda na aiki don ganin an samu saukin lamarin

Ekiti - An samu tashin hankali da rudani a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Lahadin da ta gabata saboda fargabar ramuwar gayya biyo bayan kisan da aka yi wa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar, Tope Ajayi ranar Asabar.

Ajayi, wanda mamba ne na kungiyar ma’aikatan sufurin kan tituna ta kasa (RTEAN), an harbe shi har lahira a garin Itaji Ekiti lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC da SDP suka yi arangama a wani taron kamfen a garin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani malamin addini da matarsa, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansa

Rikicin siyasa ya barke tsakanin 'yan APC da SDP a Ekiti
Rikici a Ekiti game da kashe wani magoya bayan jam'iyyar APC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jiya ne aka shiga zaman dar dar Ado-Ekiti biyo bayan rade-radin da ake yadawa cewa shugabannin RTEAN sun hada kansu domin kaddamar da wani martani, inji rahoton Daily Trust.

Mazauna suna ci gaba da zama a gida yayin da titunan garin suka kasance ba kowa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An tattaro cewa, an tura jami’an sojojin Najeriya, ‘yan sanda da jami’an tsaro na NSCDC zuwa wasu lungunan jihar.

An jibge wasu manyan motocin yaki guda uku masu sulke da manyan motoci a wurare daban-daban na babban birnin jihar, Punch ta ruwaito.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya ce mutanensa sun samu nasarar kwantar da rikicin tare da samar da kwanciyar hankali a babban birnin Ado da sanyin safiya.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Morounkeji Adesina, da sauran shugabannin hukumomin tsaro sun yi kokarin ganin an gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba domin babu wani zabe da ya cancanci zubar da jinin dan kasa.

Kara karanta wannan

Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta

Abutu ya kara da cewa:

"Game da abin da ke faruwa a fagen siyasa, CP ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin harbe-harbe da hargitsi da aka samu, muna kuma tabbatar muku da cewa za a hukunta wadanda aka samu da laifi."

COAS ga wasu jami'ai na musamman: Kada ku ji tausayin 'yan bindiga a ko ina suke

A wani labarin, babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya umarci sabbin jami’an rundunar ‘Exercise Restore Hope II’ da aka horas su 699 da su zama maras tausayi ga masu aikata laifuka dake barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Da yake jawabi ga sojojin a sansanin horas da sojojin Najeriya da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, COAS ya ce za a tura sojojin ne a fagen daga domin yaki da miyagun laifuka da sauran ayyukan ta’addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

Ya yi nuni da cewa nasarorin da runduna ta musamman ta Restore Hope l ta samu shi ya kawo ci gaba da atisayen na tsawon makonni 16 akan ingantaccen salon yaki da kuma shirye-shiryen yaki don ci gaba da tunkarar abokan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.