COAS ga wasu jami'ai na musamman: Kada ku ji tausayin 'yan bindiga a ko ina suke

COAS ga wasu jami'ai na musamman: Kada ku ji tausayin 'yan bindiga a ko ina suke

  • Shugaban hafsun sojin kasa, Laftnar Janar Faruk Yahaya ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar Kaduna na soji
  • Rahoton da muke samu ya ce, ya bukaci sojojin da aka horar da su zama masu ragargazar 'yan ta'adda ba kakkautawa
  • COAS ya kuma kaddamar da wata husumiyar hange ta soji mafi girma a duniya, wacce aka yi a Zaria

Kaduna - Babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya umarci sabbin jami’an rundunar ‘Exercise Restore Hope II’ da aka horas su 699 da su zama maras tausayi ga masu aikata laifuka dake barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Da yake jawabi ga sojojin a sansanin horas da sojojin Najeriya da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, COAS ya ce za a tura sojojin ne a fagen daga domin yaki da miyagun laifuka da sauran ayyukan ta’addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Asirin ‘Yan ta’adda ya tonu, Dakarun Sojoji sun bankado shirin hare-haren da za a kai

Kada ku tausayawa 'yan ta'adda
Shugaban soji ga jami'ai na musamman: Kada ku tausayawa tsageru a Najreiya | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Ya yi nuni da cewa nasarorin da runduna ta musamman ta Restore Hope l ta samu shi ya kawo ci gaba da atisayen na tsawon makonni 16 akan ingantaccen salon yaki da kuma shirye-shiryen yaki don ci gaba da tunkarar abokan gaba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa jami’an runduna ta musamman za su magance barazanar masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga makiya kasa da kuma masu tayar da zaune tsaye.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yahaya ya bukaci kwamandan sashen horo da koyarwa da sauran kwamandojin rundunar sojin Najeriya da su ci gaba da horar da ma’aikata gaba daya domin inganta kwarewar sojoji da hafsoshi a kan aikin.

An gina doguwar husumiyar Soji a Zaria

A halin da ake ciki, COAS ya kaddamar da hasumiya mafi girma ta sojoji tare da tsarin horar da sojoji domin inganta dabarun yaki da horar da ma’aikata a makarantar horar da sojoji da ke Zaria.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Kwamandan makarantar, Birgediya Janar A.R Abdurrahman, ya ce hasumiya ce mafi girma a Afirka da Asiya, kuma ita ce mafi tsayi a duniya, mai tsawon kafa 60, People Gazette ta ruwaito.

Yayin da a makarantar ‘yan sandan soji da ke Basawa-Zaria, COAS ya kuma kaddamar da wani kamfen na dashen itatuwa, da shingen ajujuwa, da ofisoshi da sauran ayyuka na karfafa shirye-shiryen horarwa a makarantar soji.

Daga nan ya kaddamar da sabuwar cibiyar horar da karnuka da makarantar za ta yi amfani da su wajen ayyukan sari-ka-noke a aikin soja.

Firgici: An cafke mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

A wani labarin, Daily Trust ta rahoto cewa, rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Wakilu Ogundairo bisa zarginsa da tayar da hankalin jama'a da cewa kungiyar Boko Haram ta farmaki garin Imosan-Ijebu da ke karamar hukumar Ijebu-Ode a jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce wanda ake zargin ya yi ikrari a sakon murya ta Whatsapp da aka yada ga jama’a kan wannan lamari.

Ogundairo ya yi ikirarin cewa maharan na dauke da makamai, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin da kuma kewayensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel