Ranar Damokaradiyya: Hafsoshin Sojoji 3 Sun Yanke Jiki Sun Fadi a Eagle Square
- Ana tsaka da faretin ranar damorakadiyya a filin wasa na Eagle Square da ke Abuja, hafsoshin sojoji uku sun yanke jiki sun fadi warwas
- Babu kakkautawa jami'an tsaro da masana kiwon lafiya suka garzaya tare da kwashesu inda aka kai su inuwa kafin su farfado daga bisani
- Ana kyautata zaton tsananin zafin rana da tsayuwa a wuri dayan da suka yi ya kawo wannan matsalar, duk da babu wanda ya rasa ransa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Eagle Sqaure, Abuja - Hafsoshin soji uku da ke faretin ranar damokaradiyya a ranar Litinin a filin wasa na Eagle Square da ke Abuja sun yanke jiki sun fadi.
Ana kyautata zaton sa'o'in da suka kwashe a wuri daya tare da zafin rana ne yasa suka fadin.
The Punch ta sanar da cewa, an samu dimuwa kadan yayin da wasu jami'an tsaro da likitoci suka garzaya filin faretin tare da kwashe hafsoshin sojojin a gadon marasa lafiya kuma suka ajiye su a inuwa da ke gefen hagu da inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zaune.
Sai dai, babu wanda ya rasa ransa saboda bayan gajeren lokaci aka yi nasarar samo kansu kuma suka dawo hayyacinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shagalin bikin ya samu halartar sojojin kasa, na ruwa, na sama da 'yan sanda.
Sojojin kasa na Najeriya mata sun kayatar da filin da raye-raye na al'adu daban-daban na kasar nan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne bako na musamman, ya duba sojojin sannan aka cigaba da faretin sojoji da na 'yan sanda, The Nation ta ruwaito..
Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Sakataren tarayya, shugabannin majalisar tarayya, shugabanni hafsin sojoji da sauransu.
Buratai: Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya
A wani labari na daban, Jakadar Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanat Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya bayyana hanyoyin da za a bi don kawo karshen rashin tsaro, yana mai cewa kowa na da rawar da zai taka don kawo tsaro.
Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare
Buratai, tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasan Najeriya, ya yi magana a ranar Asabar a wani taron tsaro da aka yi na rana daya Arewa House a Abuja.
Ya ce a halin yanzu akwai kallubalen tsaro da dama a sassan kasar kamar ta'addanci a arewa maso gabas, yan bindiga da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, satar danyen mai da neman ballewa daga kasa a kudu maso kudu.
Asali: Legit.ng