Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya shiga tasku inda ya ke hango yin biyu babu bayan 'dan takarar sanata na Yobe ta Arewa ya yi mirsisi ya ki janyewa
  • An gano cewa, makusantan Lawan sun dinga matsantawa Bashir Machina, wanda ya ci zaben fidda gwani na kujerrar da Lawan yake kai, da ya janye
  • Bayanai sun nuna cewa, Lawan tare da Salihu, mataimakin shugaban APC na arewa maso gabas, suna kokarin yin karfa-karfa wurin kwace tikitin takarar

Duka biyu kenan ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan. 'Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC kuma wanda ya ci zaben fidda gwani, Bashir Machina, ya ki janyewa Lawan.

Lawan, wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa, ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar shugabancin kasa da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Atiku: Wike ya samu gagarumin goyon baya daga jiga-jigan PDP

Da farko an fara bayyana shugaban majalisar dattawan a matsayin 'dan takarar yarjejeniya na jam'iyyar, amma gwamnoni 13 na arewacin Najeriya sun yi watsi da lamarin inda suka ce ya zama dole a mika mulki kudancin kasar nan.

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan
Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC

Daily Nigerian ta tattaro cewa, tunda wanda ya yi nasaa a zaben fidda gwani na kujerar sanatan da Lawan ke kai ya ki janyewa, shugaban majalisar dattawan na matsantawa fadar shugaban kasa domin ya samu tikitin kujerarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk wani kokarin masoyan Lawan na jan hankalin Machina kan ya janyewa shugaban majalisar dattawan, ya tashi a kawai saboda 'dan takarar ya ce shi fa bai ga ta janyewa ba.

Kamar yadda majiyoyi suka ce, a sirrance aka bai wa Lawan form din INEC a hedkwatar APC domin ya cike, duk da bai mayar da kansa ba domin tantancewa kuma bai shiga zaben fidda gwanin da aka yi ba a garin Gashua na ranar 28 ga watan Mayu.

A zaben fidda gwanin, Machina wanda shi ne 'dan takara daya tilo, ya samu kuri'u 289.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

Kamar yadda majiyoyi suka sanar, Lawan tare da hadin bakin mataimakin shugaban APC na arewa maso gabas, Mustapha Salihu, suna kokarin yin karfa-karfa wurin kwace tikitin takara daga Machina.

A yayin da aka tuntubi mataimakin shugaban APC na kasa na yankin arewa maso gabas, ya ce bai taba shiga wani lamarin jam'iyyar ko hukuncinta a Yobe ba.

"Ba na shiga lamarin jam'iyyar a jihohin. Yobe tana da salon ta mabanbanci na zaben fidda gwani, wanda shi ne yarjejeniya.
"Dukkan 'yan takarar da suka siya fom a fadin kasa sun cike fom din janyewa daga takarar, wanda hakan bayani ne na cewa sun amnice da hukuncin sama da su kuma tare da amincewar masu ruwa da tsaki a jihar.
"Ina da sanin cewa, tsarin jam'iyya ne a kasar nan cewa idan 'yan takara suka rasa tikitin shugabancin kasa sai su koma kujerarsu a majalisar dattawa. Kun ga Godswilla Akpabio tuni ya karbe tikitin shi," Salihu yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng