Abokin takarar Atiku: Wike ya samu gagarumin goyon baya daga jiga-jigan PDP

Abokin takarar Atiku: Wike ya samu gagarumin goyon baya daga jiga-jigan PDP

  • Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike na kan hanyar zama abokin takarar dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar
  • Wike ya ta samun goyon baya daga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a majalisar wakilai
  • Suna ganin Wike ya cancanci hawa wannan matsayin saboda gudunmawar da ya baiwa jam’iyyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Alamu sun nuna cewa mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke fada aji a majalisar wakilai na iya lamuncewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, wanda ke rike da tutar shugaban kasa na jam’iyyar.

Hakan ya fito fili ne bayan wani mamba na masu ruwa da tsakin, Mista Busayo Oluwole Oke, ya bayyana cewa manyan takwarorinsa za su gana a Abuja a yau Litinin, 13 ga watan Yuni, domin yanke hukunci, jaridar The Guardian ta rahoto.

Abokin takarar Atiku: Wike ya samu gagarumin goyon baya daga jiga-jigan PDP
Abokin takarar Atiku: Wike ya samu gagarumin goyon baya daga jiga-jigan PDP Hoto: Nyesome Wike, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Oke, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar wakilai kan asusun gwamnati, ya yi bayanin cewa mambobin da suka hada da masu yiwa jam’iyyar biyayya a fadin yankunan kasar shida, sun rigada sun yanke shawarar tsayar da Wike bayan duba gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jam’iyyar.

Jaridar ta nakalto Oke yana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mu a zauren majalisar wakilai, karkashin inuwar jam’iyyarmu mai albarka ta PDP za mu hadu a ranar Litinin a Abuja don marawa takarar gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike baya a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasar jam’iyyarmu.
“Muna ta zuba idanu kan dukkanin ayyukansa a jam’iyyarmu tsawon shekaru. Mun kuma tantance kokarinsa a dukkan bangarori na rayuwa, kuma mun ga dukkan abubuwan da jam’iyyar ke bukata don lashe zaben shugaban kasa na 2023 a tattare da shi. Da jagorancin dan takararmu na shugaban kasa, Atiku Abubakar muna da karfin gwiwar a kansu su biyun.

“Duniya ta san nasarorin da Wike ya samu a matsayin gwamnan jihar Rivers kuma yana sama da saura a kasar. Ya kasance mutum mai gwagwarmayar tabbatar da tsarin tarayya na gaskiya, wanda baya nuna kabilanci, kuma mai kare kundin tsarin mulkin mu.
“Yayin da muke mutunta yancin dan takarar shugaban kasa na zabar mutumin da yake so, shawarar da ya dauka na tuntubar sauran mutane abun yabawa ne, kuma alama ce ta dan damokradiyya na gaskiya.
“Masu ruwa da tsakin za su gana da dan takararmu na shugaban kasa don sanar da shi matsayinmu nan take.”

Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari

A wani labarin, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba, jaridar The Cable ta rahoto.

Tinubu dai shine ya yi nasarar lashe tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben fidda gwaninta da ya gudana a Eagle Square a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel