Masu Garkuwa Da Mutane Sun Bi Shugaban CAN Har Gida Sun Sace Shi a Plateau
- Masu garkuwa da mutane sun bi shugaban kungiyar CAN na karamar hukumar Jos ta Gabas, Rabaran James Kantoma har gida sun sace shi
- Wani mazaunin unguwar Angware, Silas Joshua ya tabbatar da sace malamin addinin yana mai cewa sunyi kokarin taka wa yan bindigan birki amma suka fara harbe-harbe da bindiga
- Alabo Alfred, Kakakin yan sandan Jihar Plateau ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce sun tura jami'ansu zuwa unguwar da nufin ceto Rabaran din
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Plateau - Yan bindiga sun sace limamin cocin Katolika na St Anthony a garin Angware a karamar hukumar Jos, Rabaran James Kantoma, wanda kuma shine shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN, a karamar hukumar.
The Punch ta rahoto cewa an sace Kantoma a gidansa da ke garin a daren ranar Lahadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin garin Angware, Silas Joshu, ya tabbatar wa The Punch da sace malamin addinin a Jos a ranar Litinin.
Joshua ya ce:
"Lokacin da yan bindigan suka akfa garin a daren, gidan Rabaran Fadan suka wuce nan take.
"Wasu matasa a unguwar, da suka ji hayaniyar, sun yi kokarin dakatar da yan bindigan har sun bi sahunsu amma yan bindigan suka fara harbe-harbe har suka tsere da shi."
Shugaban CAN na Jihar, Polycarb Lubo, shima ya tabbatar da sace malamin addinin, yana mai cewa abin bakin ciki.
Lubo ya ce:
"Tunda yan bindigan suka sace Rabaran Fadan, ba mu ji komai daga gare su ba har zuwa yau da safe. Abin bakin ciki ne. Muna addua kada wani abu ya same shi duk inda ya ke. Yaushe za a dena sace mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ba tare da magance matsalar ba?".
Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare
Kakakin yan sandan Jihar, Alabo Alfred, da aka tuntube shi ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce an tura jami'ansu zuwa garin don ceto shi da kama wadanda suka sace shi.
Asali: Legit.ng