2022: Wainar da su shugaba Buhari ke toyawa a Abuja yau, a bikin ranar dimokradiyya

2022: Wainar da su shugaba Buhari ke toyawa a Abuja yau, a bikin ranar dimokradiyya

  • A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura Eagle Square domin halartar taron ranar dimokradiyya
  • A ranar 12 ga watan Yuni ne Najeriya ke murnar fara mulkin dimokradiyya, tun bayan da sojoji suka mayar da mulki hannun tsarin
  • Batutuwa na ci gaba da fitowa daga Abuja a bikin da ake gudanarwa a yau dinnan, an samu halartar manya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya dura dandalin Eagle Square da ke Abuja domin halartar taron faretin ranar dimokaradiya ta 2022, Channels Tv ta ruwaito.

Faretin wani atisaye ne na shekara-shekara da ake gudanarwa domin girmama dawowar al'ummar kasar kan turbar mulkin farar hula da kuma tunawa da dadin romon dimokradiyyar Najeriya.

Jiga-jigan kasar nan sun taru domin murnar ranar dimkoradiyya
2022: Wainar da su shugaba Buhari ke toyawa a Abuja a yau, a bikin ranar dimokradiyya | Hoto: independent.ng
Asali: UGC

An sanar da zuwan shugaba Buhari ne ta hanyar gaisuwar ban girma, wanda ke nuni da fara atisayen a hukumance a babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

Kafin isowar shugaban, an ga jami'ai na gaisuwa ga manyan jami'an Sojin kasar, inda suke nuna girmamawa cikin salo irin na soja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka kuma an yi gaisuwar ban girma ga hafsoshin tsaro da Sufeto-Janar na rundunar ‘yan sanda, da kuma gaisuwa ga tsofaffin shugabannin kasa da mataimakan shugaban kasa da sauran manyan baki.

Wadanda suka halarci filin domin tarbar shugaba Buhari sun hada da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (rtd) da Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor.

Hakazalika da ministoci da sauran mambobin majalisar ministocin shugaban kasa, 'yan majalisar dokoki ta kasa, da mambobin jami'an diflomasiyya, haka nan Independent ta ruwaito.

Filin bai wani cika kamar yadda ake zato ba, amma an ga jiga-jigan farar hula da suka hada dalibai da malamai daga makarantu daban-daban, da dama suna dauke da tutar Najeriya.

Kara karanta wannan

A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari

Ana sa ran shugaba Buhari zai duba jami'an tare da rattaba hannu kan rajistar zagayowar ranar ta dimokradiyya.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wnai labarin daban, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.