APC Adamawa: Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu

APC Adamawa: Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu

  • Tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu, yace bai amince da hukuncin kotun daukaka kara ba a zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Adamawa
  • Sai dai kuma, yace bayan tuntubar ‘yan uwa, abokan arziki da shugabannin siyasa na matakai daban-daban, ya yanke hukuncin kin daukaka karar
  • Ya sanar da cewa wannan ne karo na biyu da ya nemi tikitin amma bai samu ba, kuma yayi hakan ne domin kishin jiharsa da neman damar kawo mata cigaba

Adamawa - Nuhu Ribadu yace bashi da niyyar kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara wacce ta jaddada Aishatu Binani matsayin ‘yar takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar APC, jaridar Premium Times ta rahoto.

Binani da Nuhu Ribadu
APC Adamawa: Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Binani sanata ce dake wakiltar Adamawa ta tsakiya kuma ta lallasa Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC da Jibril Bindow, tsohon gwamnan jihar inda ta lashe zaben fidda gwani da aka yi a ranar 26 na watan Mayu.

Kara karanta wannan

NECO Zata Ta Tura jami’an DSS, NSCDC Cibiyoyin Jarrabawa A Fadin Kasar

Ribadu ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban babbar kotun tarayya dake jihar.

A hukuncin alkali Abdulaziz Anka, ya soke zaben fidda gwanin tare da bayyana cewa jam’iyyar bata da ‘dan takarar gwamna a APC a Adamawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kotun daukaka karan a ranar 24 ga watan Nuwamba tayi fatali da hukuncin babbar kotun tare da jaddada Binani matsayin sahihiyar ‘yar takarar gwamnan.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, a wasikar da yayi ga mukaddashin shugaban jam’iyyar na jihar, Ribadu yace bayan zantawa da iyalai, abokan siyasa da shugabannin siyasa a matakai daban kan mataki na gaba, ya yanke hukuncin hakura tare da rungumar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

“Abinda yafi zaburar da ni wurin son shugabantar jihar shi ne in samu damar bautawa jihata matsayin gudumawata don cigaban jihar.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu, El-Rufai da Manyan ‘Yan Siyasa Sun Girgijewa Bayan Taron Gidan Chatham a Landan

- Yace.

“Aiki ne da aka fara daga abokai da makusanta da suka yarda cewa ina da gogewar da zan iya bayar da taimako wurin cigaban jihar mu.
“Ina so in yi amfani da wannan damar wurin godiya ga magoya bayana da masu yi min fatan alheri da suka sadaukar da abubuwa da dama cikin shekarun nan.
“Wannan ne yunkuri na na biyu wurin neman tikitin. A 2019 na kawo kaina amma damar ta subuce min na zama ‘dan takarar jam’iyyar. Domin fatan alheri da manufa tagari, na ajiye komai nayi aiki tare da wanda ya samu tikitin.”

Ban yarda da hukuncin ba, Ribadu

Ribadu ya kara da cewa duk da bai amince da hukuncin ba, zai hakura a inda ake domin hadin kan jam’iyyar.

“Ban yarda da hukuncin ba amma bani da niyyar kara daukaka kara.”

- Yace.

Kotu ta kwace takarar Binani, tace APC bata da ‘dan takarar gwamna a Adamawa

Kara karanta wannan

2023: Babbar Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwani Na Ɗan Takarar Gwamna a Wata Jiha

A wani labari na daban, babbar kotun tarayya dake zama a Yola babban birnin jihar Adamawa, ta yanke hukuncin cewa APC bata da takarar gwamna a Adamawa kuma ta kwace tikitin daga hannun Aishatu Binani.

A hukuncin kotun, an samu aringizon kuri’u inda yawan kuri’u da aka saka suka zarce yawan deliget.

Asali: Legit.ng

Online view pixel