Mataimakin Shugaban kasa: Atiku gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike yake so

Mataimakin Shugaban kasa: Atiku gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike yake so

  • Jam'iyyar PDP na shawarar sanar da gwamna Nyesom Wike matsayin mataimakin Atiku a zaben 2023
  • Nyesom Wike ne ya zo na biyu a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa karkashin PDP
  • Hukumar INEC ta bada mako guda wa dukkan jam'iyyu su gabatar da sunayen yan takarar shugaban kasarsu

Abuja - Muddin ba'ayi wani sauyi ba, da yiwuwan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta sanar da Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, matsayin abokin tafiyar Atiku Abubakar.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Atiku ya yiwa Wike tayin zama mataimakinsa bayan zuwansa na biyu a zaben fidda gwanin jam'iyyar.

An tattaro cewa da tuni Atiku ya sanar da Wike matsayin mataimakinsa amma wasu gwamnoni suka nuna rashin amincewarsu da shi.

Kara karanta wannan

INEC ta baiwa Atiku, Tinubu, Kwankwaso mako 1 su mika mata sunayen mataimakansu

Kawo ranar Laraba, wasu gwamnonin daban na iyakan kokarinsu na ganin cewa an sanar da Wike.

Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom na Benue, Seyi Makinde na Oyo da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku gwamnan jihar Rivers Nyesom
Mataimakin Shugaban kasa: Atiku gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike yake so hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Tribune tace gwamnonin na kokarin shawo kan sauran takwarorinsu don amincewa da Nyesom Wike.

A baya dai Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, aka so baiwa mataimaki amma wasu gwamnoni suka ce Wike ya kamata saboda yafi karfi.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa zaman da Atiku yayi da wasu gwamnoni uku ranar Laraba alamace ta cewa Wike ake shawarar ba.

Hakazalika Shugaban jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, ya gana da gwamnonin ranar Laraba kuma bayan zaman, gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa lallai maganar wanda zai zama mataimakin Atiku aka yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel