An samu labarin abin da ya sa Fasto ya tashi babu kuri’a ko 1 a shiga takarar Shugaban kasa

An samu labarin abin da ya sa Fasto ya tashi babu kuri’a ko 1 a shiga takarar Shugaban kasa

  • Tunde Bakare ya yi wa Almajiransa a coci bayanin abin da ya sa Bola Tinubu ya doke su a APC
  • Fasto Bakare da wasu masu takarar ba su iya samun ko da kuri’a daya a zaben tsaida gwani ba
  • ‘Dan siyasar ya ce yana alfahari da rashin nasarar da ya samu, amma ya ce zai karbi shugabanci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tunde Bakare wanda shi ne babban Faston Latter Rain Assembly wanda yanzu ya koma cocin Citadel Global Community, ya nemi tikitin APC.

Amma Tunde Bakare bai samu kuri’a ko daya a zaben tsaida ‘dan takaran ba. The Cable ta rahoto Faston yana mai bayanin inda ya samu matsala a zaben.

Da yake yi wa mabiyansa jawabi a coci a ranar Lahadin da ta wuce, Bakare ya ce kan shi tsaye yake yawo duk da bai samu ko kuri’a daya a zaben ba.

Kara karanta wannan

Ba sauran hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu

Dalilin tinkaho da rashin nasararsa kuwa shi ne yadda yake siyasa mai tsabta. Faston ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben, tare da yi masa fatan alheri.

Zaben tsaida gwani

Bakare ya gabatar da jawabi mai ban sha’awa, ya na neman a gyara kasa ta yadda kowa zai amfana. Wannan bai sa ya samu kuri'ar 'yan jam'iyya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tunde Bakare ya ke cewa rashin nasararsa a zaben na APC ya nuna irin yadda yake siyasarsa. Faston bai biya kowa kudi domin ya kada masa kuri’arsa ba.

Neman takarar Shugaban kasa a APC
Zaben 'dan takaran APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta rahoto limamin cocin yana cewa bai samu tikitin jam’iyyar APC ba ne saboda ya ki yin watsi da halin kirkin da aka san shi da su.

Bakare na tinkaho da 0

“A matsayin mai neman takarar shugaban kasa a zaben jam’iyyar APC, ina mai alfahari da kasancewa wanda ya yi jawabin kafa sabuwar Najeriya.”

Kara karanta wannan

EFCC za ta damke ‘Yan takara inji Mai neman tikitin APC da ya kashe N100m, ya samu kuri’a 0

“Ba na jin kunya saboda ban yi fatali da halayen da suke da muhimmanci wajen kafa sabuwar Najeriya. A wurinmu ko ba ku kai labari ba, ba komai.”
“Shiyasa mu ke tunkaho da rashin kuri’un da mu ka samu, ya nuna rashin biyewa wani irin siyasa.

- Tunde Bakare

Tunde Bakare zai zama shugaban kasa?

Duk da bai kai labari a zaben ba, kuma ya sallamawa Tinubu, Bakare ya fadawa Almajiransa cewa shi zai zama sabon shugaban kasa a watan Mayun 2023.

Mabiya sun yi ihu a coci da fadar wannan magana, amma ba su san ta yadda hakan za ta yiwu ba.

EFCC na nan - Bakare

Kwanaki kun samu rahoto da ya ce Fasto Tunde Bakare ya hango cewa nan gaba kadan za a ga EFCC ta na neman wasu abokan takaransa a zaben APC.

A jawabin da ya gabatar wajen tsaida gwanin APC, Bakare ya ce an yi amfani da kudi wajen samun kuri’u 'ya 'yan jam'iyya domin shiga takara a 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel