El-Rufai: Yadda Muka yi da Buhari Kan 'Dan Takarar da Deliget din Kaduna Zasu Zaba
- Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya sanar da yadda suka yi da shugaban kasa kafin deliget din Kaduna su yi zaben fidda gwani
- A cewarsa, Buhari ya bukaci su yi zabi mai kyau saboda wakiltar mutane miliyan 10 na Kaduna da suke yi, amma bai basu sunan 'dan takara da za su zaba ba
- El-Rufai ya sanar da cewa, deliget din Kaduna da yawa Tinubu suka zaba, wasu sun zabi Amaechi yayin da wasu suka zabi Farfesa Yemi Osinbajo
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyna yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki bayyanawa deliget daga jiharsa wanda za su zaba a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.
Tun farko dai shugaban kasan ya sanar da cewa ba shi da 'dan takarar da ya ke goyon baya a zaben fidda gwani, wanda daga bisani Bola Ahmed Tinubu ya ci.
A yayin jawabi ga Channels Tv a shirin Siyasarmu A Yau, El-Rufai ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da deliget cewa su zabi wanda suke so.
"A da yawa daga cikin jihohinmu, kuri'un deliget sun rarrabu ne," El-Rufai yace.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Kafin in je yin jawabin karshe ga deliget din Kaduna, na samu shugaban kasa kuma na tambaye shi ko ya yanke hukunci kan wanda za su zaba? Ya ce, na fada muku, ku je ku yi zabe, ku zabi kowanne 'dan takara daga cikin 'yan takara biyar da gwamnonin APC suka zaba.
“Na ce masa, shugaban kasa, deliget din Kaduna naka ne, za ka yi ritaya kuma Kaduna za ka dawo da zama. Don haka za ka iya fada min wanda ka ke so daga cikin su biyar din. Sai shugaban kasan ya ce, ina son su biyar din duka.
"Na ce, me toh zan sanar da deliget din Kaduna. Ya ce, ka sanar da su cewa su zabi zabinsu, suna wakiltar mutane miliyan 10 ne daga jihar Kaduna. Babban nauyi ne kuma su sauke shi yadda ya dace ta hanyar zaben wanda ya dace.
“Toh daga nan ban san yadda deliget din Kaduna suka yi zabe ba. Amma daga labarin da na samu bayan zaben, da yawa daga cikinsu Asiwaju suka zaba, wasu sun zabi Amaechi kuma wasu sun zabi Farfesa Yemi Osinabjo."
Bayan zaben fidda gwani, Ahmad Lawan ya shiga ganawa da ma'aikatan majalisa
A wani labari na daban, a yanzu haka dai shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan yana wata ganawar sirri da shugabannin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya.
An fara taron ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Juma’a lokacin da shugaban majalisar dattawan ya isa harabar majalisar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, duk da cewa shugabannin sun gayyaci manema labarai zuwa taron, amma mambobin sun ki barin manema labarai shiga harabar.
Asali: Legit.ng