Da dumi-dumi: Bayan zaben fidda gwani, Ahmad Lawan ya shiga ganawa da ma'aikatan majalisa

Da dumi-dumi: Bayan zaben fidda gwani, Ahmad Lawan ya shiga ganawa da ma'aikatan majalisa

  • Shugaban majalisar dattawa ya shiga ganawa da shugabannin ma'aikatan majalisar dokokin kasar nan
  • Ya shiga ganawa da su ne domin dinke wasu maganganu da ke da alaka da kudaden albashi da alawus alawus na ma'aikata
  • Wannan ganawa dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC

Abuja - A yanzu haka dai shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan yana wata ganawar sirri da shugabannin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya.

An fara taron ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Juma’a lokacin da shugaban majalisar dattawan ya isa harabar majalisar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, duk da cewa shugabannin sun gayyaci manema labarai zuwa taron, amma mambobin sun ki barin manema labarai shiga harabar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutum 3 Da Suka Kashe Yar Shugaban Afenifere, Ta Wanke Kakakin Miyetti Allah

Hukumar ta PASAN ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Litinin din da ta gabata sakamakon gazawar da mahukuntan majalisar suka yi na cika sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna da ta shiga da ma’aikata kan biyan basussukan albashi da alawus alawus.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel