2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal

2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya nuna karfin gwiwar cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu zai kayar da Atiku a jiharsa ta Adamawa
  • Babachir ya ce jam'iyyarsu ta APC na da yan amana a fadin Adamawa kuma za su kawowa Tinubu jihar kamar yadda suka kawowa Buhari
  • Sai dai kuma kan batun zama mataimakin Tinubu, tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce Allah bai ce masa ya nemi kujerar ba

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa Bola Tinubu zai kayar da Atiku Abubakar a jihar Adamawa a babban zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da Atiku, wanda zai daga tutar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sune manyan yan takara a zaben kasar mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: A karon farko, Bola Tinubu ya tabo magana game da wanda zai zama Mataimakinsa

Ana sanya ran Atiku wanda ya kasance dan asalin Adamawa ya kawo jihar a zabe mai zuwa amma tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce sam hakan ba mai yiwuwa bane.

2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal
2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

A wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Lawal ya ce APC na da yan amanarta a fadin jihar, don haka Atiku zai sha kashi a 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Muna nan, kuma mune yan Adamawa da za mu kawowa Bola Tinubu jihar kamar yadda muka kawo wa Buhari yayin da suka yi takara da Atiku, Adamawa ta kawowa Goodluck Jonathan yayin da Atiku ke takara, saboda haka ba sabon abu bane.
“Muna da yan amanarmu a fadin jihar, jiharmu ce, kuma mun san halinmu, Bola Tinubu zai lashe jihar Adamawa.
“Ko da shi Tinubu ya kai labari ko bai kai ba, Allah kadai ya sani, amma za mu yi aiki kan haka kuma mun yarda cewa muna da kayan aiki, muna da arzikin na kaya da hankali don isar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

“Tinubu mutumin kirki ne. Yana da kirki sosai, kuma kuna bukatar jin hakan daga bakin wasu mutane da ya taimakawa, da dama a duk fadin kasar nan.
“Ya dauki nauyin mutane a Taraba, a Adamawa, a Gombe; shi mutum ne da ya taimaki kusan duk wani dan siyasa a fadin kasar nan.”

Da aka tambaye shi ko yana fatan a zabe shi a matsayin abokin takarar Tinubu, Lawal ya ce baya takarar wannan kujera, jaridar TheCable ta rahoto.

Ya ce:

“Bana cikin tseren neman kujerar. Allah bai ce mani na nemi wannan matsayin ba.”

Hudubar da Goodluck Jonathan ya yi wa Atiku, Tinubu, Obi, Kwankwaso da suka samu takara

A wani labarin, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga masu takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da su guji raba kan al’umma.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan kira ne a jawabin da ya fitar a shafinsa na Twitter, yana mai taya wadanda suka samu takara murnar lashe zaben gwani.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Da yake magana a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni 2022, tsohon shugaban na Najeriya ya ce akwai bukatar a gujewa kazamin kamfen domin a cigaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng