Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne wanda ya yi nasarar zama ‘dan takarar APC a zaben 2023 mai zuwa
- Fitaccen ‘dan siyasar ya samu kuri’u fiye da 1000, ya sha gaban kowa a zaben tsaida gwani na APC
- Bola Ahmed Tinubu ya samu tikiti ne da taimakon Gwamnoni da wasu manyan kusoshin jam’iyya
Abuja - Bayan tsawon lokaci ana ta gwagwarmaya da fafutuka, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama ‘dan takarar shugaban kasan Najeriya a jam’iyyar APC.
A wani rahoto da ya fito daga Vanguard a ranar Alhamis, an yi bayanin yadda ‘dan siyasar ya yi nasarar samun yin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Gwamonin jam’iyyar APC sun yi bakin kokarinsa na ganin Bola Tinubu ya zama ‘dan takara a 2023 bayan zaman da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari.
Kungiyar gwamnonin Arewa ta dauki matsaya cewa akwai bukatar shugabanci ya koma kudu.
Abdullahi Adamu da Ahmad Lawan
A gefe guda, ana zargin shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi kokarin kakabawa jam’iyya mai mulki Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takaransu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan ya sa a ranar Lahadi, gwamnonin jihohin su ka nemi su hadu da Abdullahi Adamu da ‘yan majalisar NWC, amma sai kowa ya rasa inda Adamu ya shiga.
Rahotanni sun nuna an bi shugaban jam’iyyar har gida, aka nuna masa matsayar gwamnonin Arewa. Tun daga nan maganar zaben Lawan ta fara lafawa.
Kokarin Majalisar NWC
Su ma ‘yan majalisar gudanarwa na APC NWC sun nuna ba su gamsu da sanarwar da Adamu ya bada ba, suka fito fili suka shaidawa Duniya ba su tare da shi.
Legit.ng Hausa ta samu labari shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ya barranta NWC daga sanarwar Adamu, ya ce ba su tsaida magana a kan hakan ba.
Aikin gama ya gama!
Bayan nan sai wadannan gwamnoni su ka nunawa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da ke alhakin kada kuri’u cewa su zabi Bola Tinubu a zaben fitar da gwanin APC.
A wajen zaben ‘dan takarar, ‘ya ‘yan jam’iyya daga kusan duka jihohin Najeriya sun zabi Tinubu ne illa irinsu Dave Umahi da Yahaya Bello wanda su na takara.
Mutum 7 sun janye takara
An kuma ji labarin cewa daga cikin kusoshin APC, Godswill Akpabio, Kayode Fayemi, Badaru Abubakar, da Roberts Ajayi Borroffice sun taimaki takarar Tinubu.
Ibikunle Amosun da Mrs Uju Ken Ohanenye su ma sun janye takararsu, hakan ya sa Bola Tinubu ya yi galaba. Wanda ya zo na biyu a zaben ya kare ne da kuri’u 316.
Asali: Legit.ng