EFCC za ta damke ‘Yan takara inji Mai neman tikitin APC da ya kashe N100m, ya samu kuri’a 0
- Tunde Bakare yana cikin wadanda ake gani sun gabatar da jawabi mafi kyau a zaben ‘dan takaran APC
- Fasto Tunde Bakare ya hango cewa nan gaba kadan za a ga EFCC ta na neman wasu abokan takaran na sa
- A jawabin da ya gabatar wajen tsaida gwanin APC, Bakare ya ce an yi amfani da kudi wajen samun kuri’u
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Fasto Tunde Bakare ya yi wa jam’iyyarsa ta APC mugun baki, inda ya ce za a nemi a kama wasu daga cikin ‘yan takararta.
A ranar Laraba, 8 ga watan Yuni 2022, aka rahoto Tunde Bakare yana mai cewa EFCC za ta nemi kama wasu da suka nemi tikiti a APC.
Limamin cocin na Citadel Global Community ya yi wannan bayani sa’ilin da yake gabatar da jawabi wajen zaben ‘dan takaran 2023.
Legit.ng Hausa ta fahimci mutane sun yaba da jawabin da Faston ya gabatar, har ana ganin da a ce wannan ne mizani, da ya samu takara.
Shahararren malamin addinin kiristan ya nuna fushinsa karara kan yadda aka yi aiki da kudi wajen samun nasara a zaben gwani.
“Da yawa daga cikin wadannan ‘yan takaran, nan da wani lokaci, hukumar EFCC za ta fara bibiyarsu.” - Tunde Bakare.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Su wanene da laifi?
‘Dan siyasar bai fadi sunan wani daga cikin abokan hamayyarsa da ya ba ‘yan jam’iyya kudi da nufin samun kuri’unsu a zaben ba.
Bakare ya shaida cewa bai iya samun haduwa da ‘yan jam’iyyar APC da ke kada kuri’a a zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa ba.
Bakare ya rungumi zamani
Faston ya aikawa masu zaben sakon wayar salula ne domin su tsaida shi a matsayin ‘dan takara.
Sannan Bakare ya ce dole duk wani mai niyyar zama shugaba a Najeriya ya rungumi fasahohin zamani wajen siyasa da shugabanci.
Da yake jawabin neman goyon baya, ya dauki tsawon minti daya ya nemi jama’a su yi tsit domin makokin wadanda aka kashe a coci.
Nasarar Tinubu da walakin - PDP
A yammacin Laraba aka ji labari PDP tayi magana a kan zaben ‘dan takaran shugaban kasa da jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar.
Jawabin da Debo Ologunagba ya fitar ya nuna PDP ta na zargin an yi amfani da kudi wajen tsaida Bola Tinubu takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng