Tsohon Ministan Buhari ya buge da cacar-baki a filin zaben ‘dan takarar shugaban kasa

Tsohon Ministan Buhari ya buge da cacar-baki a filin zaben ‘dan takarar shugaban kasa

  • Rahotanni sun ce Rotimi Amaechi ya nemi ya samu takaddama da wasu a wajen zaben ‘dan takara
  • A halin yanzu jam’iyyar APC ta na kokarin fito da wanda zai yi mata takarar shugaban Najeriya
  • Rotimi Amaechi yana cikin masu neman tikiti, saura kiris hayaniya ta kaure tsakaninsa da wasu

Abuja - A wasu bangarorin, an samu labari cewa kai ya yi zafi a wajen zaben tsaida gwanin ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an hangi Rotimi Amaechi ya na daga murya, abin har ya kai ga gardama a farfajiyar Eagle Square a Abuja.

Har zuwa yanzu ba a san abin da ya jawo tsohon Ministan sufurin ya samu sabani da jama’a ba.

Ana zargin Rotimi Amaechi wanda yana cikin masu neman takarar shugaban kasa a APC ya samu takkadama ne da wasu wakilai a zaben na APC.

Kara karanta wannan

Peter Obi da Atiku ba su yi barci da wuri ba ba, sun yi magana a kan zaben ‘dan takaran APC

Da mutane su ka fara cika a lokacin da tsohon gwamnan na Ribas yake daga muryarsa da karfi, sai aka ga ya bar wurin zuwa inda mutanensa ke zaune.

Har zuwa yanzu dai babu wani labarin rigima da aka samu a wajen zaben ‘dan takaran na APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi a gaban kwamitin APC Hoto: @ChibuikeAmaechi
Asali: Twitter

Zabe ya tafi lafiya kalau

A lokacin da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na jihar Kano su ke kada kuri’unsu ne sai aka dakatar da zabe saboda gudun a samu rudani wajen tattara sakamako.

A wadanda suka fito neman takarar, mutane uku su na dauke da ‘Ahmad’ a sunansu, wannan ya sa aka dakatar da zaben domin gudun a samu rudani.

Ni ba tsoho ba ne - Amaechi

Da Rotimi Amaechi ya je gabatar da jawabi, an ji yana kokarin jan hankalin masu kada kuri’a da cewa shekarunsa 57, ma’ana bai tsufa da shugabanci ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karyata labarin ‘sharrin’ da ake yi masa ana tsakiyar zaben ‘Dan takaran APC

Bugu da kari, tsohon Ministan ya yi ikirarin ya fi kowane mai neman takara samun kwarewa domin ya rike kujerar ‘dan majalisa, gwamna da ta Minista.

Amaechi ya yi bayanin yadda ya rike shugaban kungiyar gwamnoni, kuma ya jagoranci yakin neman zaben Muhammadu Buhari sau biyu a 2015 da 2019.

'Yan adawa sun yi martani

Dazu mu ka samu labari ‘Dan takaran jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi kira ga matasa su duba rayuwarsu a yau da yadda suke rayuwa kafin zuwan APC.

Shi ma Atiku Abubakar bai kwanta da wuri ba a daren yau, an ji shi a Twitter yana cewa gwamnatin APC ba ta cika alkawarin da ta yi wa jama’a ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel