Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takara a jam'iyyar su Adamu Garba

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takara a jam'iyyar su Adamu Garba

  • Jam'iyyar YPP ta kammala zabenta na fidda gwanin dan takarar shugaban kasa gabanin babban zaben 2023 mai zuwa
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan kammala zaben fidda gwanin APC da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja
  • An zabi Prince Malik Ado-Ibrahim a matsayin wanda zai gwabza da su Atiku da Tinubu a zaben na 2023 mai zuwa

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wanda ya kafa tafiyar Reset Nigeria Initiative, Prince Malik Ado-Ibrahim, ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar Young Progressives Party, YPP.

Ya samu nasarar kayar da takwararsa Mrs. Ruby Issac da kuri'u sama da 66 sannan Ruby Issac ya samu kuri'u 4 kawai.

YPP ta tsayar Malik a matsayin dan takarar shugaban kasa na zaben 2023
Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a jam'iyyar su Adamu Garba | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Akwai kusan deliget 74 na jam'iyyar da aka tantance, amma 70 ne kadai suka kada kuri'a.

Idan dai za a iya tunawa dai tsohon jigo a jam’iyyar APC, Adamu Garba, ya kamata ya kasance cikin ‘yan takarar shugaban kasan, amma ya janye daga takarar, inda ya ce ya hadiya burinsa na hada kan matasa.

Kara karanta wannan

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu A Zaben Fidda Gwanin APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani bidiyon da kafar labarai ta Channels Tv ta yada ya nuna cikakken lokacin da ake gudanar zaben fidda gwanin jam'iyyar.

Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

Tsohon gwamna jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A zabensa na faako tun bayan barin muli a 2007, Tinubu yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Tinubu ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u sama da 1,271.

Wanda ya zo na biyu shine tsohon Gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316.

Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

A wani labarin, tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka yi a ranar Laraba.

A halin yanzu jam'iyyar NNPP tana gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasar ta a filin Moshood Abiola Stadium da ke Abuja.

Kwamkwaso ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasar na NNPP ne bayan daligets daga jihohi sun sahale masa da baki kamar yadda The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.