2023: Kamar Yadda Ta Faru a APC, Yar Takarar Shugaban Kasa Mace a SDP Ta Janye Wa Wani

2023: Kamar Yadda Ta Faru a APC, Yar Takarar Shugaban Kasa Mace a SDP Ta Janye Wa Wani

  • Cesnabmihilo Dorathy Nuhu-Aken’Ovia, yar takarar shugaban kasa a jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta janye takararta
  • Dorathy Nuhu-Aken’Ovia ta janye ne kuma ta umurci magoya bayanta su mara wa Prince Adewale Adebayo baya a zaben cikin gida na jam'iyyar
  • Yar takarar ta ce ta yanke shawarar janye wa ne saboda jam'iyyarta ta yanke shawarar mika tikitin takarar zuwa yankin kudu kasancewarta mai biyayya sai ta janye

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Awanni kafin fara gangamin taron jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a ranar Laraba a Eagle Square a Abuja, yar takarar shugaban kasa, Cesnabmihilo Dorathy Nuhu-Aken’Ovia, ta janye daga takarar, rahoton Daily Trust.

Yar takarar shugaban kasar na 2023, ta janye daga takarar ta kuma ta goyi bayan Prince Adewole Adebayo, ta bukaci magoya bayanta su jefa masa kuri'a.

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

2023: Kamar Yadda Ta Faru a APC, Yar Takarar Shugaban Kasa Mace a SDP Ta Janye Wa Wani
2023: Yar Takarar Shugaban Kasa Ta SDP Ta Janye, Ta Fadi Dalilin Yin Haka. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Dalilin da yasa Nuhu-Aken’Ovia ta janye takara

A taron manema labarai da ta kira, ta ce ta janye daga takarar ne a lokacin da jam'iyyar ta yanke shawarar mika mulki ga kudu kasancewarta mai biyayya ga jam'iyya, sai ta janye.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewa dukkan magoya bayanta da ofisoshinta za su koma goyon bayan kamfen din Adebayo.

"Jam'iyya ce farko. Ni mai biyayya ne ga jam'iyya. Abin da jam'iyya na ta ce zan bi. Kuma nauyi ya rataya a kai na da sauran yan jam'iyya su tabbatar jam'iyya ta yi nasara a zabe mai zuwa.
"Na yanke shawarar goyon bayansa ta hanyar sadaukar masa da dukkan kayan kamfen di na don ya samu nasara," in ji ta.

Prince Adewale Adebayo, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar da ta janye wa ya jinjinawa matakin da takwararsa ta yi, yana mai cewa abin koyi ne.

Kara karanta wannan

2023: Jami'aiyyar NNPP mai kayan marmari zata zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa yau a Abuja

Ya ce ya kamata a karfafa wa mutane irin ta gwiwa su rika fitowa su yi wa kasa hidima.

Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Su 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari

A wani rahoton, wasu daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a APC sun yi watsi da sunayen yan takar da gwamnoni suka mika wa Shugaba Buhari don ya zabi magajinsa daga cikinsu, rahoton Tribune.

Wadanda ba su yarda da hakan ba akwai Gwamnan Cross Rivers Ben Ayade; Tsohon Karamin Ministan Ilimi, Emek Nwajiubu; Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, Tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da dan kasuwa Tein Jack-Rich.

Shugaban Kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong ne ya tabbatar da jerin sunayen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel