Deleget 774 zasu zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP yau a Abuja
- A yau Laraba 8 ga watan Yuni, 2022, jam'iyyar NNPP zata gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a Abuja
- Jam'iyyar tace Deleget 774 daga jihohin Najeriya 36 ne zasu kaɗa kuri'un su don tabbatar da ɗan takara a MKO Abiola Stadium
- Jam'iyyar ta sha alwashin cewa ta shirya sharewa yan Najeriya hawayen su ta hanyar tsayar da mutanen kirki
Abuja - Deleget 774 na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ake sa ran zasu taru a Filin Moshood Abiola da ke birnin tarayya Abuja domin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.
Tribune Online ta rahoto cewa Deleget ɗin daga jihohin Najeriya 36 zasu taru yau 8 ga watan Yuni a wurin babban taro na musamman na jam'iyyar NNPP ta ƙasa.
Kakakin jam'iyyar NNPP ta ƙasa, Dakta Agbo Major, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a babbar Sakatariya ta ƙasa da ke birnin Abuja.
Agbo ya ce NNPP ta zamo wata sabuwar amarya a siyasar Najeriya yayin da mutane suka rungume ta kuma suka fahimci manufarta na inganta goben Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jami'iyyar ta yi kira ga yan Najeriya kwansu da kwarkwata su yi rijistar katin zaɓe kuma su killace shi a wuri mai tsaro, kana su tabbata a babban zaben 2023 sun dangwala wa NNPP mai alamar kayan marmari.
Mista Agbo ya ce:
"Shugabannin jam'iyyar mu sun jima suna kokarin yadda za'a ci da ƙasar nan gaba, da kuma cigaba da shirya dabarun gudanar da babban taron fidda gwani wanda zai gudana ranar 8 ga watan Yuni, 2022 a MKO Abiola Stadium."
"Muna tsammanin wakili ɗaya daga kananan hukumomi 774 da muke da su a faɗin Najeriya, hakan na nufin Deleget 774 zasu yanke ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar mu."
Zamu tabbatar mun tsayar da yan takara nagari - NNPP
Dakta Agbo ya ƙara da cewa jam'iyyar NNPP ta hana kanta bacci don tabbatar da cewa ta zakulo yan takara nagari, waɗan da zasu cika muradan mutane kuma su lashe zaɓe.
NNPP ta kuma buƙaci yan Najeriya ka da su yarda da yan siyasar da zasu sayi kuri'un su kamar yadda suka sayi na Deleget a wasu zaɓukan fidda gwani da kowa ya gani a ƙasar nan.
A wani labarin na daban kuma Dirama yayin da Jami'an tsaro mata biyu suka buɗa, suka ba hammata iska a filin taron APC
Wasu jami'an tsaro mata su biyu sun buɗa a filin taron APC, sun bai wa hammata iska har sai da aka shiga tsakanin su.
Wani bidiyo ya bayyana yadda jami'ar hukumar yan sanda da kuma yar uwarta ta hukumar Cibil Defence suka dambace a Eagle Square.
Asali: Legit.ng