Zaben fidda gwanin APC: Deliget din Jigawa ya yanki jiki, ya fadi matacce
- Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben fidda gwanin APC, jigo a jam'iyyar ya kwanta dama
- An ruwaito cewa, deliget daga jihar Jigawa ya yanki jiki ya fadi saboda bugun zuciya da safiyar yau dinnan
- Duk da cewa majiya ta tabbatar da faruwar lamarin, har yanzu ba a bayyana lokacin jana'iza ba tukuna
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin wakilan jam'iyyar APC na Jigawa Alhaji Isah Baba Buji ya rasu yayin da yake wurin taron zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar a Abuja.
Ya fadi ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Talata a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja.
Marigayin dai shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Jigawa ta tsakiya, inji rahoton jaridar The Nation.
An ce ya fadi ne a lokacin da yake shirin zuwa dandalin Eagle Square, inda za a yi zaben fidda gwani tare da wasu wakilai daga jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC na Jigawa Malam Bashir Kundu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ka zabi daya daga cikinmu: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari
A wani labarin, 'yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC daga yankin Kudu maso Gabas sun rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), domin bai wa yankin Kudu maso Gabas damar fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
A wani kwafin wasikar da wakilin Punch ya samu a ranar Talata, ‘yan takarar sun bukaci Buhari ya sa baki a yayin zaben domin samar da “shugaba mai kyau”.
Wasikar na dauke da sa hannun Ikeobasi Mokelu, tsohon ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Dokta Ogbonnaya Onu; karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da Mrs. Ken Uju-Ohanenye.
Asali: Legit.ng