Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun fara harba wa Yan Jarida barkonon tsohuwa a Eagle Square

Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun fara harba wa Yan Jarida barkonon tsohuwa a Eagle Square

  • A kokarin jami'an tsaro na tarwatsa mutanen da suka taru a Kofar shiga wurin taron APC sun harba barkonon tsohuwa
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da suka haɗa da yan jaridu da wasu Deleget sun yi kokarin turjiya ga jami'an
  • Hakan yasa tilas jami'an suka ɗauki matakin harba barkonon kuma hakan ya yi sanadin guduwar kowa a wurin

Abuja - Har zuwa yanzun Jami'an tsaro sun hana yan jarida da wasu Delegets shiga filin Eagles Square wurin babban taron jam'iyyar APC nazaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

Jami'an tsaron ɗauke da bindigu kuma cikin ɗamar aiki sun umarci yan jaridar waɗan da aka tantance su bar kofar shiga wurin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Filin taron APC.
Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun far harba wa Yan Jarida barkonon tsohuwa a Eagle Square Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan matsa wa yan jarida da sauran mambobin APC su bar wurin, jami'an tsaron sun kuma harba barkonon tsohuwa, hakan ya tilas wa mutane guduwa neman mafaka.

Kara karanta wannan

Bayan zaftare yan takara zuwa biyu, An matsawa Osinbajo ya janye don tabbatar da magajin Buhari

Daily Trust ta rahoto cewa tun safe yan jarida ke dakon takardar shedar sahalewa su gudanar da aikin su na ɗakko labarai daga kwamitin midiya na taron karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da safe jami'an tsaro suka hana yan jarida shiga

Tun mako biyu kafin zuwan wannan rana, gidan jaridu suka kammala shirye-shirye tare da ware ma'aikatan da zasu tura don aikin nemo labarai a wurin taron.

Hakan ya sa manema labarai suka zauna a kusa da kofar shiga filin taron yayin da suke jiran kwamitin midiya ya gabatar musu da katin aiki don samun damar shiga.

A halin yanzun komai ya kankama an gama tantance Deleget baki ɗaya kuma sun nemi wuri sun zauna yayin da ake jiran isowar shugaba Buhari.

A wani labarin na daban kuma Babbar Kotu ta soke zaɓen fidda ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: APC Za Ta Jefa Kanta Cikin Fitina Idan Ta Hana Yin Takara a Zaben Fidda Gwani

Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abakalike, ta soke zaben fidda gwanin PDP na ɗan takarar gwamnan jihar Ebonyi wanda aka sake shirya wa.

Punch ta rahoto cewa Kotun ta yanke cewa zaɓen fitar da ɗan takara wanda ya gudana a ranakun 5 da 6 ga watan Yuni, 2022 ya saɓa wa doka kuma ta soke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel