Yanzu nan: Masu neman kujerar shugaban kasa a APC sun ragu, an bar mutum 2 kacal
- Ana kokarin fitar da wanda zai zama ‘dan takarar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC
- Kabiru Ibrahim Gaya ya nuna takarar za ta zama tsakanin mutum biyu ne a zaben tsaida gwani
- Wadanda suka isa matakin karshe su ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Bola Tinubu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Bayanin da mu ke samu shi ne an sake rage masu neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Gidan talabijin na Channels TV ya rahoto Kabiru Ibrahim Gaya yana cewa an yi waje da sauran wadanda suke neman tikiti.
‘Yan jarida sun tambayi Kabiru Gaya a game da kokarin da ake yi a APC na rage masu harin tikiti a zabe mai zuwa na 2023.
Tsohon Gwamnan yake cewa a zaben ‘dan takara irin wannan, a kan dauki mataki a mintin karshe, kuma sai ta zauna.
An yarda a kai takara Kudu - Kabiru Gaya
“Saboda haka abin da mu ka sani shi ne shugabancin Najeriya ya koma Kudu, wannan shi ne matsayata fiye da shekaru biyu da suka wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuma a wannan matsaya mun yarda da wannan, mun amince takara ta je Kudu domin a samu mataimaki daga yankin Arewa, sai a ci zabe.
Na yi imani cewa za mu cin ma matsaya, ko da ba mu yarda a kan mutum daya ba, za mu tsaya a kan mutane biyu ko uku da za su yi takara.”
- Sanata Kabiru Gaya
Mutum 2 suka rage
An rahoto Sanatan na kudancin Kano yana cewa maganar da ake kai shi ne Bola Tinubu da Yemi Osinbajo suka rage a ‘yan takaran.
‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa za a samu ‘dan takarar shugaban kasa na 2023 ne daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Har ila yau, Gaya ya bayyanawa manema labarai cewa akalla mutum biyu suka janye takararsu, su na marawa Yemi Osinbajo baya.
Sanata Ken Nnamani yana cikin wadanda za a bada sanarwar su na tare da Osinbajo a zaben fitar da gwanin da za a fara an jima.
Batun Ahmad Lawan
Sanata Gaya bai yarda a ba Sanata Ahmad Lawan takara a zaben 2023 ba, ganin cewa Muhammadu Buhari ya fito ne daga Arewa.
A cewarsa, da haka ne al’umma za su yarda jam’iyyar za ta tafi da kowane bangare na kasar nan.
Tinubu ya sha gaban kowa
Dazu kun ji labari cewa lura da yadda abubuwa ke tafiya a APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi gaba a wajen samun takarar shugabancin Najeriya.
Gwamnonin APC ke da wuka da nama a jihohin da suke mulki, maganar da ake yi shi ne Tinubu ya fi sauran masu neman takara kafa a APC.
Asali: Legit.ng