Baba-Inna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Adamawa

Baba-Inna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Adamawa

  • A karo na farko, jam'iyyar People Redemption Party (PRP) ta tsayar da dan takara da zai daga tutarta a zaben gwamnan jihar Adamawa na 2023
  • Ibrahim Baba-Inna ne ya yi nasarar lashe tikitin jam'iyyar a zaben fidda gwanin da aka gudanar inda ya samu kuri'u 64
  • Ya kayar da abokin hamayyarsa, Alhaji Mustapha Umar, wanda ya dawo jam'iyyar daga APC bayan ya sha kaye a hannun Sanata Aishatu Binani

Adamawa - Ibrahim Baba-Inna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar People Redemption Party (PRP) a jihar Adamawa bayan ya kayar da Alhaji Mustapha Umar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

An tattaro cewa wannan shine karo na farko da jam’iyyar PRP ke tsayar da wanda zai daga tutarta a zaben gwamna a jihar.

Kara karanta wannan

Hadimin Ganduje da ya rasa kujerarsa kan sukar Buhari ya samu takarar Gwamnan Kano

Baba-Inna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Adamawa
Baba-Inna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Adamawa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Baba-Inna ya samu kuri’u 64 wajen kayar da Umar wanda ya sauya sheka zuwa PRP daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bayan ya sha kaye a hannun yar takarar gwamna ta APC, Sanata Aishatu Binani.

Jaridar The Sun ta nakalto Baba-Inna a jawabinsa yana fadin:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zan so na mika godiyata ga abokin karawa na a wannan zaben fidda gwanin, Alhaji Mustapha Umar. Yadda ya gudanar da lamuransa sun taimaka sosai wajen fitar da kyakyyawan sakamako cike da wayewa. Wannan al'amari ne mai kyau ga jam'iyyarmu, kuma ina so in gaya masa cewa duk wasu kofofin hadin gwiwarmu a bude suke gare shi. Don Allah, ka zo mu tsara makomarmu tare.
“Wannan sakamakon a yau ya tabbatar da hasashena game da karfin jam'iyyarmu na yin nasara a zabe mai zuwa."
“Ya ku mambobin PRP, wannan ita ce damar mu na ba jihar Adamawa shugabanci na zamani wacce za ta shafi al’umma. Wannan ita ce damarmu na gabatar da kyawawan manufofin jam’iyyarmu da suka dade da yantar da jihar Adamawa gaba daya daga mulkin mallaka.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

“Zamu iya sake farfado da kasarmu kuma mu sauya tunanin mutanenmu don su ga cewa ana yi da su. Za mu iya baiwa al’ummar Adamawa mai inganci fiye da yadda muke da su a yanzu.”

2023: Jam'iyyar NRM Ta Zabi Dan Takararta Na Shugaban Kasa

A wani labarin, Mazi Okwudili Mwa-Anyajike, ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar National Rescue Movement (NRM) na babban zaben shekarar 2023.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ya zama dan takarar na NRM ne a babban zaben jam'iyyar da aka yi na 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

A zaben da aka yi tsakanin yan takarar shugaban kasa su tara, Okwudili ya samu kuri'u 184 cikin fiye da 200 da aka tantance cikin daligets 300, rahoton Blueprint.

Asali: Legit.ng

Online view pixel