2023: Jam'iyyar NRM Ta Zabi Dan Takararta Na Shugaban Kasa

2023: Jam'iyyar NRM Ta Zabi Dan Takararta Na Shugaban Kasa

  • Jami'yyar National Rescue Movement (NRM) ta zabi Mazi Okwudili Mwa-Anyajike a matsayin dan takararta na shugaban kasa a 2023
  • Mwa-Anyajike ya yi nasarar zama dan takarar ne bayan ya samu kuri'u 184 cikin fiye da 200 da aka kada yayin zaben jam'iyyar da aka yi
  • Shugaban jam'iyyar na kasa, Ambasada Isaac Chigozie Udeh ya bukaci sauran yan takarar su mara wa wanda ya yi nasara baya don ceto Najeriya

FCT, Abuja - Mazi Okwudili Mwa-Anyajike, ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar National Rescue Movement (NRM) na babban zaben shekarar 2023.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ya zama dan takarar na NRM ne a babban zaben jam'iyyar da aka yi na 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kano 2023: Sirikin Kwankwaso, Abba Gida-Gida ya tabbata 'dan takarar gwamna a NNPP

2023: Jam'iyyar NRM Ta Zabi Dan Takararta Na Shugaban Kasa
2023: Jam'iyyar NRM Ta Zabi Mazi Okwudili Mwa-Anyajike a matsayin dan takararta na shugaban kasa a 2023. Hoto: @PMLOnline.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A zaben da aka yi tsakanin yan takarar shugaban kasa su tara, Okwudili ya samu kuri'u 184 cikin fiye da 200 da aka tantance cikin daligets 300, rahoton Blueprint.

Bayan Barista Musa Isiaka da Barista Obidike Okoli sun bude taron, shugaban kwamitin amintattu, BOT, Sanata Saidu Muhammed Dansadau ya shawarci daligets din su zabi wanda ya fi cancanta saboda jam'iyyar tana aikin ceto kasa ne daga halin da ta shiga.

Shugaban na BOT ya kuma bukaci masu neman takarar su taru su mara wa wanda ya yi nasara baya bisa tsarin jam'iyyar.

A jawabinsa na maraba, Shugaban jam'iyyar na kasa, Ambasada Isaac Chigozie Udeh ya bukaci dukkan yan takarar su saka Najeriya a gaba domin ba mu da wata kasa da ta fi Najeriya.

Kafin fara zaben, yan takarar shugaban kasar Prof. Benedicta Egbo; Ambassador Sam Emiaso; Barry Avotu Johnson; Dr. Emeka Mandela Ukaegbu; Dr. Solomon Uchenna Winning; Francis Ikechukwu Igbo; Vincent Antony Ubani; Senator Ibrahim Yunusa; da Mazi Okwudili Mwa-Anyajike duk sun nemi goyon bayan daligets din suna masu alkawarin ceto Najeriya daga halin da ta shiga idan an zabe su a 2023.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Bayyana Yankin Da Magajinsa Zai Fito a 2023

Kaduna: Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Zabi Tsohon Sanata A Matsayin Dan Takarar Gwamna

A wani rahoton, Sanata Suleiman Hunkuyi, a jiya ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bayan samun kuri'un daligets guda 732, rahoton Leadership.

Dan takarar na NNPP zai fafata da Mohammed Ashiru na jam'iyyar PDP da Uba Sani na jam'iyyar APC da wasu yan takarar gwamnan daga wasu jam'iyyu a zaben na 2023.

Hunkuyi ya wakilci mazabar Kaduna North a majalisar dattawa a majalisa zubi ta 8 karkasin APC kafin ya koma PDP a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel