Maganar tsaida ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar lalama ta balbalce ana gobe zaben APC

Maganar tsaida ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar lalama ta balbalce ana gobe zaben APC

  • Maganar fito da ‘dan takarar shugaban Najeriya ta hanyar yin maslaha a jam’iyyar APC ya ci tura
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taro sau hudu a kan maganar magajinsa, bai yi nasara ba
  • Tun da maslaha ba ta yiwu ba, za a shiga zaben fitar da gwani domin a tsaida ‘dan takaran 2023

Abuja - Yunkurin fito da ‘dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 ta hanyar yin maslaha a jam’iyyar APC mai mulki ya gagara yiwuwa.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa maganar ta shiririce ne a yammacin ranar Litinin.

Duk da kan gwamnonin Arewa ya hadu a kan cewa daga kudu ya kamata a samu ‘dan takara, ba a iya tsaida magana a kan wanda za a ba tikiti ba.

Jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi ta yin zama a garin Abuja domin dinke sabanin da ke tsakaninsu, amma a karshe ba a iya haduwa a kan shafi guda ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC

Jaridar ta samu labari daga majiya mai karfi cewa idan har ba a iya fito da ‘dan takara ta maslaha ba, za a ba kowa damar shiga zaben tsaida gwani.

Idan hakan ta yiwu, ‘ya ‘yan jam’iyya 2, 322 daga kananan hukumomi 774 ne za su tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga cikin mutum kusan 23.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kasa
Buhari da Gwamnonin Arewa Hoto: @buhari.sallau
Asali: Facebook

An tsara zaben fitar da gwanin ne ta yadda kowace karamar hukuma ta na da ‘ya ‘yan jam’iyya uku wadanda za su kada kuri’arsu a Eagle Square.

Daga Asabar zuwa jiya, jam’iyyar APC mai mulki tayi ta kokarin ganin ba sai an shiga filin zabe ba.

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zauna da masu neman takara a jam’iyyar APC, ya kuma bukaci su sasanta da junansu cikin lalama.

Wannan umarni da shugaban Najeriyan ya bada ya jawo aka yi ta yin taro iri-iri da nufin ganin kai ya hadu tsakanin ‘yan siyasan yankunan kasar nan.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai

Kwamitin da aka nada

Buhari ya kira taro sau hudu a kan maganar, ya nada wani kwamiti na mutum uku da ya kunshi; Abdullahi Adamu, Atiku Bagudu da Boss Mustapha.

Amma wata majiya ta ce kwamitin bai iya yin komai ba, a karshe Buhari ya fitar da jawabi yana cewa a shiryawa zaben fitar da gwani a ranar Talata.

Gwamnonin Arewa

A ranar Litinin aka ji labari Gwamnonin Arewacin Najeriya su na nan a kan matsayarsu na cewa sai an ba kudu takara a 2023, ba su tare da Ahmad Lawan.

Ana haka ne sai aka ji shugaban APC yana cewa Ahmad Lawan ne 'dan takaran jam'iyya, amma shugaban kasa ya nuna babu ruwansa da wannan magana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel