Kaduna: Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Zabi Tsohon Sanata A Matsayin Dan Takarar Gwamna
- Sanata Suleiman Hunkuyi ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a zaben 2023 a Jihar Kaduna
- Hukunyi ya yi nasarar zama dan takarar na NNPP ne bayan daliget guda 732 sun sahalle masa ya wakilci jam'iyyar a 2023
- Ana fatan Hukunyi zai fafata da Uba Sani na jam'iyyar APC, Mohammed Isa Ashiru na jam'iyyar PDP da wasu yan takarar a 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Sanata Suleiman Hunkuyi, a jiya ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bayan samun kuri'un daligets guda 732, rahoton Leadership.
Dan takarar na NNPP zai fafata da Mohammed Ashiru na jam'iyyar PDP da Uba Sani na jam'iyyar APC da wasu yan takarar gwamnan daga wasu jam'iyyu a zaben na 2023.
Hunkuyi ya wakilci mazabar Kaduna North a majalisar dattawa a majalisa zubi ta 8 karkasin APC kafin ya koma PDP a 2019.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan majalisar ya fice daga PDP ya koma NNPP a 2022.
A yayin da ya zama Hunkuyi dan takarar NNPP, Shugaban Kwamitin Zabe, Mohammed Bello Ma'aji, ya ce cikin daligets 756, an tantance 732, adadin kuma ya isa su yi zaben fidda gwanin, rahoton The Punch.
Dukkan daligets 732 sun amince da zaben Hunkuyi
Ma'aji ya tambayi daligets din har sau uku su tabbatar sun amince da zaben Suleiman Hunkuyi a matsayin dan takarar NNPP, kuma suka amsa da cewa eh.
An yi zaben na Hunkuyi ne karkashin sa idon Kwamishinan INEC, Dr Asmau Sani Maikudi da tawagarta daga hukumar Zabe wato INEC daga ofishinsu na Kaduna.
A jawabinsa na amincewa, Hunkuyi ya tunatar da gwamnati mai ci yanzu da hakkin da ke kanta na samar da tsaro da walwala da muhalli ga mutanen kasar.
Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC
A wani rahoton, dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya bayyana dalilinsa na barin inda ake zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.
Sharada ne dan takara daya da ya nuna rashin amincewarsa akan gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a farkon watan Mayu, rahoton The Cable.
A wata takarda wacce Daily Nigerian ta saki ranar Juma’a, Sharada ya ce dakyar shi da wasu mabiyansa su ka sha daga harin da aka kai musu.
Asali: Legit.ng