Babban abin da ya sa Gwamnonin Arewa ba su so Lawan ya zama Shugaban kasa inji Uzor Kalu

Babban abin da ya sa Gwamnonin Arewa ba su so Lawan ya zama Shugaban kasa inji Uzor Kalu

  • Orji Uzor Kalu ya na zargin Gwamnonin Arewa da nunawa Ahmad Lawan hassada a zaben 2023
  • ‘Dan majalisar ya ce Gwamnonin ba su son Lawan ne saboda zai toshe masu damar da suke hange
  • Kalu yake cewa idan Sanatan ya karbi mulki, Gwamnonin nan sun rasa kujerar mataimaki kenan

Abuja - Orji Uzor Kalu wanda shi ne shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya ya zargi gwamnonin Arewa da yi wa Ahmad Lawan hassada.

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce hassada ce ta sa wasu gwamnoni ba su goyon bayan takarar Ahmad Lawan.

The Cable ta bibiyi hirar, ta rahoto Kalu yana cewa ana yi wa yankin da Lawan ya fito bakin ciki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan dan takarar da yake so ya gaje shi

“Mafi yawan mutanen nan su na hassada da jin haushin mutumin da ya fito daga karamar al’umma yana neman ya zama shugaban kasa.”
“Kuma wannan shi ne dadin tsarin damukaradiyya; wannan ne abin da ya kamata mu rika gani – mutum irin Lawan ya karbi shugabanci.”
“Wanda bai taba zama gwamna ba, ya fado kwatsam, ya zama shugaban kasa.” - Uzor Kalu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sen. Orji Uzor Kalu
Jigon APC na kasa, Orji Uzor Kalu Hoto: @OUKtweets
Asali: Twitter

An rahoto ‘Dan majalisar yana cewa gwamnonin sun bayyana abin da suka fadawa shugaban kasa, amma ba su iya yin bayanin abin da shi ya fada masu ba.

Bugu da kari, Kalu ya ce an yi wa wasu alkawarin gwamnonin Arewa kujerar mataimakin shugaban kasa, don haka saboda burinsu su ke wannan magana.

Ba kishin kasa ba ne - Kalu

“Wadannan mutane su daina hassada. Maganar son rai ce. Wasu su na son zama shugaban kasa, wasu su na son zama mataimakin shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

Zaben Ahmad Lawan zai barka Gwamnonin APC, sun ce dole mulki ya koma Kudu a 2023

“Sun san cewa da zarar an zabi Ahmad Lawan yanzu, kamar yadda aka yi, an rufe masu kofa.
“Su na son zama shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa. Ra’ayin kan su, an yi wa wasunsu alkawarin kujerar mataimakin shugaban kasa.”

- Uzor Kalu

Kalu yace gwamnoni biyar aka yi wa alkawari za a basu mataimakin shugaban kasa, ya kuma ce yana da hujjojinsa, don haka ya nemi su nuna kishin kasa.

Matsayar APC ko Shugaban APC?

Maganar Kalu ta biyo bayan shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya bada sanarwar Sanata Ahmad Lawan ne ‘dan takaran jam’iyya na shugaban kasa.

Sanatan na jihar Abia yake cewa babu yadda za ayi Sanata Abdullahi Adamu ya dauki wannan matsaya ba tare da ya zauna da Mai girma shugaban kasa ba.

Orji Uzor Kalu yake cewa masu adawa da wannan matsaya da jam’iyya ta dauka na fito da ‘dan takara ta maslaha, su na ‘hassada da bakin ciki’ ne kawai.

Kara karanta wannan

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

Asali: Legit.ng

Online view pixel