Deliget sun fusata, suna bukatar Adamu ya yi murabus daga shugabancin APC

Deliget sun fusata, suna bukatar Adamu ya yi murabus daga shugabancin APC

  • Akwai yuwuwar Sanata Abdullahi Adamu zai fuskanci barazanar rasa kujerarsa a matsayin shugaban jam'iyyar APC nan kusa
  • A halin yanzu, wasu 'yan jam'iyyar sun fara kira ga sauke 'dan siyasar da aka haifa a Nasarawa bisa matakin da ya dauka a jiya
  • Sanata Adamu ya sanar da Ahmad Lawan a matsayin 'dan takarar jam'iyyar bayan sulhun da aka yi a jam'iyyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT,Abuja - The Nation ta ruwaito yadda wasu wakilan zabe suka bukaci shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, da ya yi hanzarin sauka daga kujerarsa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, bukatar sauke shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi kamari ne bayan ya bada sanarwan Ahmad Lawan a matsayin 'dan takarar jam'iyya kafin zaben fidda gwanin jam'iyyar da zai gabata a ranar Talata 7 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Ana Dab da Fara Zaben Fidda Gwani, Buhari ya Aika Muhimmin Sako ga Deliget

Deliget sun fusata, suna bukatar Adamu ya yi murabus daga shugabancin APC
Deliget sun fusata, suna bukatar Adamu ya yi murabus daga shugabancin APC. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hukuncin da Sanata Abdullahi ya yi na da hatsari

Yayin martani, mutane da dama sun ce dabi'un Adamu sun nuna yadda yake hidima ga wasu tsirarun 'yan siyasa wadanda suka hada da wasu musu fadi a ji na fadar shugaban kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Akwai hatsari Adamu ya cigaba da shugabantar APC.
"Da irin wannan abun kunyar da ya nuna, Adamu ya fito karara ya bayyana yadda bai cancanta da shugabancin APC ba.
"Abun kunya ne a ce mutumin da Buhari ya farfado da shi daga talaucin siyasa a watan Maris yayin da ya nada shi shugaban jam'iyyar APC na kasa shi ne ke kokarin rusa wannan dai jam'iyyar cikin watanni uku."

Wata wakiliyar zaben jam'iyyar, Bintu Ibrahim daga jihar Neja, ta ce:

"A halin yanzu ban gamsu Adamu ya cigaba da rike mukamin shugaban APC ba."

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na arewa maso yamma, Dr. Salihu Lukman ya yi suka game da tsarin gudanar da mulkin Adamu, wanda ya siffanta a matsayin mai kare martabar kalilan din mutane.

Haka zalika, shugaban kungiyar APC wanda ya dade da barin jam'iyyar, Alhaji Buba Galadima ya siffanta Adamu inda ya ce:

"Idan da shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne dake tuna sharrin da akai masa a baya, da ba zai ko yi musabaha da Adamu ba a yau, ballantana har ya nadasa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa bayan irin miyagun abubuwan da ya yi wa Buhari a lokacin da Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa a ANPP yayin da Adamu yake gwamnan jihar Nasarawa."

Shugabancin kasa a 2023: Ni ne muryar matasa da mata, Gwamna Yahaya Bello

A wani labari na daban, kafin zuwan zaben 2023, 'dan takarar shugabancin kasa kuma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Lahadi ya ce shi ne muryar matasan kasar nan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC

Gwamnan ya bayyana hakan a shirin Siyasa na gidan talabijin na Channels, sa'o'i kadan kafin a fara zaben fitar da 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC.

"A watan Yunin shekarar nan zan cika 47. Har yanzu ina da kuruciya, ni ne muryar matasan kasar nan, muryar mata, muryar nakasassu kuma muryar 'yan Najeriya ba tare da dubi da addini, yanki ko kabila ba saboda mun kwatanta hakan a jihar Kogi," gwamnan yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel