Lawan, Ekweremadu, Gbaja da Sanatoci da ‘Yan Majalisan da suka fi kowa dadewa a Majalisa
- A siyasar Duniya, a kan samu ‘yan siyasan da suka shafe shekara da shekaru su na aikin majalisa
- ‘Yan majalisa ba su da wa’adi, za su iya daukar tsawon rayuwarsu a kan kujera idan har sun ci zabe
- A Najeriya akwai ‘yan majalisar tarayyar da sun yi fiye da shekaru 20 su na wakiltar mazabunsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
1. Nicholas Mutu
Tun da aka dawo mulkin farar hula a shekarar 1999, Hon. Nicholas Mutu ne yake wakiltar mutanen Bomadi/Patani na jihar Delta a majalisar tarayya.
Nicholas Mutu ya rike shugabancin kwamitin Neja-Delta tun daga 2009 zuwa 2019. Punch ta ce shi ya fi kowane ‘dan majalisa yawan ayyuka na NDDC.
2. Ahmad Lawan
A zaben 1999 ne Ahmad Ibrahim Lawan ya zama ‘dan majalisar yankin Bade/Jakusko. A wannan kujera ne ya yi shekaru takwas a ANPP har zuwa 2007.
A zaben na 2007 ne Dr. Ahmad Lawan ya zama Sanatan Arewacin jihar Yobe. Tun lokacin nan ya zama Sanata, a 2019 ya karbi iko da majalisar dattawan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
3. Femi Gbajabiamila
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila shi ne shugaban majalisar wakilan tarayya na kasa a yau. ‘Dan siyasar yana kan wa’adinsa na biyar kenan a kujerar majalisa.
A 2003 Femi Gbajabiamila ya zama ‘dan majalisar yankin Surulere I, tun wancan lokaci bai fadi zabe ba. Bayan shekara 16 ya zama mutum na hudu a kasar.
4. Muhammad Ali Ndume
Shi ma Muhammad Ali Ndume ya zama ‘dan majalisar wakilai na yankin Chibok/Damboa/Gwoza ne a 2003, ya yi shekara takwas yana rike da wannan mukami.
A 2011 aka zabe shi a matsayin Sanatan kudancin Borno, har yau kuma shi ne a kan kujerar.
5. Ike Ekweremadu
Ba a taba yin wanda ya dade yana jagorantar majalisar dattawa kamar Sanata Ike Ekweremadu ba. Shi ma ya zo majalisa ne a 2003, kuma ya dade ana yi da shi.
Ike Ekweremadu ya shafe shekaru 12 a jere a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
6. James Manager
Ba zai yiwu ayi maganar Santaocin da suka dade ba tare da an ambaci James Manager. Sanatan zai cika shekara 20 yana wakiltar mutanen kudancin Delta a 2023.
7. Leo Ogor
Wani ‘dan siyasa da ya tare a majalisar tarayya tun 2003 shi ne Leo Ogor. A shekara mai zuwa ‘dan majalisar na Isoko-North/Isoko-South zai cika shekara 20.
8. Alhassan Ado-Doguwa
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa ya zo majalisa ne a 2007. Ana tunanin yana harin shugaban majalisa idan ya zarce a 2023.
9. Mohammed Monguno
Wani wanda ya dade a majalisa kuma yana neman shugabanci shi ne Hon. Mohammed Monguno mai wakiltar Marte/Monguno/Nganzai, sau biyar ana rantsar da shi.
10. Kabiru Ibrahim Gaya
A shekarar 2007 ne Kabiru Ibrahim Gaya ya zama Sanatan kudancin Kano a majalisar dattawa. A zabe mai zuwa shi ne zai sake tsayawa jam’iyyar APC takara a Kano.
11. Enyinnaya Abaribe
Bayan rikicinsa da Gwamnansa a 2007, Enyinnaya Abaribe ya zama Sanatan Abia ta kudu a majalisa, shekararsa 15 kenan bai motsa daga majalisar dattawan ba.
12. Yakubu Dogara
Tsohon shugaban majaliar wakilai, Yakubu Dogara yana cikin wadanda suka ga jiya da yau a majalisa, tun 2007 yake wakiltar Bogoro, Dass da Tafawa Balewa.
13. Mukhtar Betara
Wani ‘dan majalisan Borno a jerin shi ne mai wakiltar mazabun Biu/Bayo/Shani, a 2007 Mukhtar Betara ya zo majalisa, kuma babu mamaki ya zarce har 2027.
14. Khadijah Abba-Ibrahim
Babu macen da ta dade a majalisa kamar Khadijah Abba-Ibrahim mai wakiltar Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa, sau biyar ta na cin zabe a yankinta a Yobe.
PDP ta shiga rudu a Legas
Akwai shirin gudanar da wani sabon zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta ke yi a jihar Legas. Idan za a tuna, dazu mu ka fitar maku da wannan labarin.
A yau ake tunanin za a zabi wadanda za su yi wa PDP takarar ‘yan majalisa a jihar Legas bayan rusa zaben ‘yan takarar majalisar tarayya da aka yi a Mayu.
Asali: Legit.ng